Wani Kirista A Iraqi Ya Ki Siyar Wa Wanda Ya Kona Qur'ani A Sweden Kaya, Ya Fadi Dalili
- Wani Kirista dan asalin kasar Iraqi da ke zaune a Sweden ya yi abin burgewa bayan kin siyar wa Momika lemon kwalba
- Salwan Momika wanda dan Iraqi ne ya kona Qur'ani a bakin masallacin Stockholm a ranar bikin babbar sallah
- Kiristan ya ce ya ki siyar wa Momika lemon kwalbar ce don nuna bakin cikinsa akan abin da ya aikata wa Musulmai
Stockholm - Wani Kirista dan Iraqi mai suna Ibrahim Sirimci ya ki siyar da lemon kwalba ga mutumin da ya kona Qur'ani a Sweden.
Ibrahim wanda ke zaune a Sweden ya yi hakan ga Salwan Momika don nuna rashin jin dadinsa akan aika-aikar da ya yi.
Ibrahim na siyar da kayan abinci ne a shagonsa inda ya nadi faifan bidiyon lamarin a lokacin da ya ke faruwa tare da yadawa a kafofin sadarwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani Kirista a cikin shagon ya barranta kansa da Momika
Har ila yau, wani Kirista a cikin shagon ya bayyana wa Momika cewa ya bata musu rai kamar yadda ya batawa Musulmai, cewar Anadolu Ajansi.
Ya ce:
"Ni Kirista ne dan Iraqi amma ka yi abin kunya da cin mutunci ga Musulunci, ka bata mana rai kamar yadda ka yi wa sauran mutane."
Mai kantin, Sirimci ya bayyana cewa lokacin da ya gane Momika ne ya zo siyan kaya a shagonsa, sai ya yanke shawarar kin siyar masa da kaya.
Ya bayyana yadda ya ki siyar masa da kaya a shagon
A cewarsa:
"Ya zo kantina don siyan lemon kwalba, da na gane shi sai na ce masa, kai ne ka kona Qur'ani, don haka ba zan siyar maka ba."
Momika dan asalin kasar Iraqi ya kona Qur'ani ne a ranar babbar sallah a bakin babban masallacin Stockholm da ke Sweden tare da samun kariya daga 'yan sanda.
TRT Hausa ta tattaro cewa, Momika ya sake yaga Qur'ani da tutar kasar Iraqi a ranar 20 ga watan Yuli a birnin Stockholm.
Fastoci A Arewacin Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Kona Qur'ani Da Aka Yi A Sweden
A wani labarin, Gamayyar limaman coci a Arewacin Najeriya sun yi Allah wadai da kona Qur'ani a Sweden.
Wani dan asalin kasar Iraqi da ke zaune a Sweden ya kona Qur'ani a bakin masallacin birnin Stockholm a ranar sallah.
Kungiyar ta ce abin takaici ne da kuma cin zarafi, inda suka ce a shirye suke su kare martabar Qur'ani.
Asali: Legit.ng