Hotuna Sun Yadu Na Daya Daga Cikin 'Yan Matan Chibok Da Ta Kubuta A Hannun Boko Haram, Ta Samu Mijin Aure
- 'Yan kungiyar Boko Haram sun sace daliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a shekarar 2014
- Daya daga cikin 'yan matan da suka kubuta, Joy Bishara ta tsallaka zuwa kasar Amurka tare da kammala digiri
- Joy Bishara daga bisani ta samu mijin aure dan asalin kasar Amurka da suke shirin yin aure a can
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Daya daga cikin 'yan matan Chibok da Boko Haram suka kama a shekarar 2014 ta samu masoyi a Amurka bayan ta kubuta daga hannunsu.
Joy Bishara kamar yadda Legit.ng ta tattaro ta samu mijin aure ne a kasar Amurka bayan tsawon lokaci da ta dauka a kasar.
Daily Trust ta tattaro cewa Joy Bishara da 'yar uwarta Lydia Pogu sun tsallaka Amurka ne bayan sun tsira daga hannun 'yan Boko Haram.
Bishara ta kasance karkashin kulawar wani mazaunin Amurka
Sun kasance a karkashin kulawar wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Emmanuel Ogebe kafin Gwamnatin Tarayya ta karbi ikon kulawar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Premium Times ta ruwaito cewa Bishara ta kammala digiri a jami'ar Southeastern a shekarar 2021.
Idan ba a mantaba a shekarar 2014 'yan ta'addan Boko Haram sun sace 'yan matan Chibok 276 a karamar hukumar Chibok da ke jihar Borno.
'Yan matan Chibok fiye da 100 ne ke hannun 'yan Boko Haram
Sace sun ke da wuya 57 daga cikinsu suka dira daga cikin motar da aka sace su kafin kai su sansanin 'yan ta'addan.
Yayin da wasu daga cikinsu jami'an sojoji suka kubutar da su daga hannun 'yan ta'addan.
A yanzu haka 'yan matan Chibok fiye da 100 suna hannun Boko Haram da ba a san halin da suke ciki ba
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
Sojoji Sun Ceto Dalibar Makarantar Chibok Dauke Da Juna Biyu
A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya ta kubutar da wata daga cikin 'yan matan Chibok da Boko Haram suka sace.
Dalibar mai suna Hauwa Maltha mai shekaru 26 ta kubuta ne daga hannun 'yan ta'addan bayan sojojin sun kai samame a Lagarta.
Jami'an sojin sun kubutar da Hauwa da 'yarta karama a ranar Laraba 21 ga watan Afrilu bayan ta shafe shekaru tara a hannun 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng