‘Yan Sanda Sun Bazama Farautar Wadanda Suka Sace Boka A Anambra
- Wani shahararren boka ya gamu da tsautsayi bayan masu garkuwa da mutane sun sace shi a dakin otal
- An sace Chinedu Nwangwu ne a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli da dare tare da kashe masu tsaronshi mutum biyu
- Mai hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da sace bokan ga 'yan jaridu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Anambra - Masu garkuwa sun sace wani shahararren boka a jihar Anambra mai suna Chinedu Nwangwu da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki.
An sace Chinedu ne a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli bayan harbe wasu masu tsaronshi su biyu a kokarin sace shi.
Bokan ya sanu wurin nuna arzikinsa da kuma karfin ikon da yake da shi na tsafi a kafafen sada zumunta, cewar TheCable.
Har yanzu ba a san halinda bokan ya ke ciki ba
Punch ta tattaro cewa an sace bokan ne a dakin otal dinsa na Triple P da ke Oba a ranar Lahadi da dare.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wata majiya ta tabbatar cewa har yanzu ba a san inda bokan ya ke ba tun bayan sace shi da aka yi da misalin karfe 11:30 na dare, Vanguard ta tattaro.
Majiyar ta ce:
"An sace Akwa Okuko Tiwaraki da misalin karfe 11:30 na dare a dakin otal dinsa bayan bindige wasu masu tsaronsa guda biyu har lahira."
'Yan sanda sun tabbatar da sace bokan, sun bazama ceto shi
Mai hulda da jama'a na rundunar a jihar, DSP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar hakan inda ya ce an sace bokan ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi.
Duk da cewa wasu daga cikin magoya bayan bokan sun bayyana cewa an sako bokan kamar yadda suke yada wani faifan bidiyo a jiya Litinin 24 ga watan Yuli.
Rundunar 'yan sanda ta musa labarin cewa an saki bokan inda ta ce babu wani kamshin gaskiya a cikin sakin bokan, cewar Daily Trust.
Mummunan Karshe: Boka Ya Mutu Ya Na Lalata Da Uwargidar Wani Fasto
A wani labarin, wani boka ya yi mummunan karshe bayan ya mutu ya na lalata da wata matar fasto a jihar Ekiti.
Rahotanni sun tabbatar cewa bokan ya aikata hakan ne a ranar Alhamis 5 ga watan Janairu a Ikere Ekiti da ke jihar.
Fadayomi Kehinde wanda boka ne da aka fi sani da Ejiogbe ya mutu ne yayin da yake wani otel a garin na Ikere Ekiti tare da matar faston.
Asali: Legit.ng