Jami'ar Abuja Ta Samar Da Dokar Da Za Ta Tilasta Wa Dalibai Mallakar Kamfani Kafin Kammala Digiri

Jami'ar Abuja Ta Samar Da Dokar Da Za Ta Tilasta Wa Dalibai Mallakar Kamfani Kafin Kammala Digiri

  • A kokarinta na samar wa matasa abin dogaro da kai, jami'ar Abuja ta samar da sabuwar doka don rage rashin aikin yi
  • Mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Abdul Rasheed Na'Allah shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu a Abuja
  • Ya ce kowa ne dalibi doka ce kafin kammala digiri sai ya yi rijistar kamfani da hukumar CAC da zai dogara da kansa

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban jami'ar Abuja, Farfesa Abdul Rasheed Na'Allah ya ce yanzu doka ce dalibi sai ya mallaki kamfani kafin kammala jami'ar.

Farfesan ya ce hakan na daga cikin dokokin makarantar kafin dalibi ya samu damar kammala digiri.

Jami'ar Abuja Ta Kafa Dokar Da Za Ta Tilasta Wa Dalibai Mallakar Kamfani Kafin Kammala Digiri
Mataimakin Shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Na'Allah Ya Ce Sun Samar Da Dokar Da Za Ta Tilasta Wa Dalibai Mallakar Kamfani Kafin Kammala Digiri. Hoto: Gold Educational Service.
Asali: Facebook

Yayin bayyana irin nasarorin da suka samu a lokacinsa ga 'yan jaridu, Na'Allah ya ce sun yi wani yunkuri na sauya akalar jami'ar ta fannin ilimi da sana'o'i, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

Ya ce dokar za ta taimakawa dalibai don dogaro da kansu

Ya ce sun hada gwuiwa da hukumar kasuwanci ta Abuja don inganta tsarin karatu tare da koya wa dalibai yadda za su yi rijistar kamfani ba tare da dogaro da aikin gwamnati ba, cewar Leadership.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Wannan masana'antar kullum su na koyawa dalibai sabbin abubuwa a tsarin koyarwa.
"Yanzu haka fiye da dalibai 1000 sun yi rijistar kamfanonin su da hukumar CAC.
"Sannan dalibai da ke kusa da ajin karshe ke gudanar da kamfanonin da suka yi rijista don sanin makaman aiki.
"Abin da muke fadawa daliban mu shi ne ba takardar shaida kawai zamu ba ku ba, zamu ba ku damar samar wa kanku aiki da wasu jama'a."

Ya bayyana yadda dokar ta ke akan kowa ne dalibi

Kara karanta wannan

Jami’ar Danfodiyo Ta Dage Jarrabawarta a Karo Na Hudu, Ta Fadi Dalili

Ya ce mafi yawan daliban sun yi rijistar kamfanonin su, idan aka je hukumar CAC za a shaida haka.

Ya kara da cewa:

"Ku sani babu wani dalibi da zai kammala digiri ba tare da kamfani mai rijista ba, doka ce.
"Kafin kammala karatun za ka gudanar da kamfanin don tabbatar da kwarewarka akai tunda za ka yi rijistar ne shekara daya ko biyu kafin kammala karatun.

Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta

A wani labarin, wata daliba ta bankawa dakin kwanan dalibai wuta a jami'ar Abuja da ke Najeriya.

Rahotanni sun tattaro cewa an gano wani faifan bidiyo inda dalibar ke barazanar daba wa duk wadanda ke kokarin kashe wutar wuka.

Dalibar ta fara cinnawa katifarta wuta a dakin kafin daga bisani ta kona dakin gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel