“INEC Ta Yi Kuskuren Tsaida ‘Dan APC a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna”
- Bernard Ifeanyi Odoh ya ce ba za ta yiwu a ce jam’iyyar APC ta lashe zaben Gwamnan Ebonyi ba
- ‘Dan takaran na APGA ya fadawa kotun zabe cewa Francis Nwifuru ‘dan jam’iyyar PDP ne ba APC ba
- Lauyan Farfesa Odoh ya tunawa Alkalai doka ba ta hana yin takara a jam’iyya ba sai ‘dan jam’iyya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ana shari’a da Bernard Ifeanyi Odoh wanda ya yi wa jam’iyyar APGA takarar Gwamna a zaben jihar Ebonyi a kotun sauraron karar zabe.
A farkon makon nan The Nation ta rahoto Farfesa Bernard Ifeanyi Odoh yana mai ikirarin an yi kuskure wajen ba Gwamna Francis Nwifuru nasara.
A cewar Bernard Odoh, ba sabon Gwamnan kuma ‘dan takaran APC a zaben bana ne ya yi galaba ba, yana mai ganin hukumar INEC ta tafka kuskure.
Odoh ya tafi kotun zabe
Odoh ya na kalubalantar sakamakon zaben a kotun da ke zama a Abuja bisa zargin tun farko Francis Nwifuru bai dace ya shiga takara a APC mai-ci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesan ya ce dalilinsa kuwa shi ne Nwifuru ya yi shugaban majalisar dokoki ne a karkashin jam’iyyar PDP, a maimakon APC da ta ba shi tikiti a 2023.
Lauyan ‘dan takaran na APGA, J.S. Okutepa ya ce hukumar zabe na kasa watau INEC, ba ta da wata madogara wajen ayyana Nwifuru a matsayin Gwamna.
"'Dan PDP ne ya ci zabe a APC"
Jaridar ta rahoto Lauyan ya hakikance wanda ake cewa shi ya yi nasara a APC, ‘dan PDP ne.
Barista Okutepa ya kafa hujja da dokar zaben 2022 da kundin tsarin mulki, sun yi bayanin haramcin mutum ya shiga takara a jam’iyyar da ba ta shi ba.
To fah: Atiku ya tada hankalin Tinubu, ya fadi hujja 1 a kotu, ya ce kawai a tsige Tinubu a ba shi Najeriya
Odoh wanda ya taba rike kujerar Sakataren gwamnatin Ebonyi ya zargi INEC da yin aikin jam’iyyun siyasa a maimakon zama hukumar zabe mai adalci.
A zaben da ya gabata, Bernard Ifeanyi Odoh wanda Farfesa ne a fannin Geophysics ya yi wa APGA takarar Gwamna a jihar Ebonyi, amma bai kai labari ba.
Yanzu haka ana sauraron karar wannan zabe a Abuja, ba da dadewa ba malamin jami’ar na Nnamdi Azikiwe da ke Awka a Anambra zai san makomarsa.
Karin karatu ga tsadar rayuwa
An ji labari a shekarar 2020, N48,500 aka biya a makarantun sakandaren gwamnatin tarayya, a farkon 2023 an biya N47,000, amma yanzu ya kai N100, 000.
Bincike ya nuna ba gwamnatin Bola Tinubu tayi wa daliban sakandare karin kudin makaranta ba, Sai dai sabon shugaban kasar yana shan sukar jama’a.
Asali: Legit.ng