Muhammadu Buhari Ya Ƙara Kuɗin Makarantu, Ya Ƙyale Tinubu da Shan Sukar Jama'a
- Muhammadu Buhari ne ya yarda aka yi karin kudin karatu a makarantun sakandaren gwamnati
- Amma da yake an yi karin ne a karshen mulkin baya, yanzu Gwamnatin Bola Tinubu ake faman suka
- Gwamnatin tarayya tayi wa iyayen yara karin kudin makaranta daga N30, 000 zuwa 100, 000 a yanzu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ma’aikatar ilmi ta tarayya ta amince da karin kudin makarantun sakandaren gwamnati tun a karshen watan Mayun da ya gabata.
Legit.ng Hausa ta fahimci Muhammadu Buhari ya amince da canjin kudin makarantar a lokacin yana ofis, kafin ya mika mulki.
Sai a ranar 29 ga watan Mayu ne wa’adin gwamnatin Buhari ya cika, bayan ya shafe shekaru takwas a jere ya na kan karaga a Aso Rock.
Tinubu bai san hawa ba...bai san sauka ba
Akasin abin da mutane ke fada, ana zargin Bola Tinubu da kara kudin karantun daliban sakandaren gwamnatin da bai da hannu a ciki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk da gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin fetur a ranar farko, amma kafin sabon shugaban kasar ya shiga ofis, kudin karatun ya tashi.
Aikinsu Malam Adamu Adamu ne
Binciken Legit.ng Hausa ya tabbatar da haka, mun gano Malam Adamu Adamu ya sa hannu aka tashi kudin makarantun gwamnatin tarayya.
Darektar sashen karatun sakandare a ma’aikatar, Hajiya Binta Abdulkadir ta rattaba hannu a takardar karin kudin a madadin Ministan ilmin.
Karin da aka yi zai fi shafan masu kwana a makarantun a maimakon ‘yan je-ka-ka-dawo a sakamakon maida kudinsu ya zama N30, 000.
Sannan ‘yan aji 1 da 4 (JSS I da SSS I) ne za su rika biyan kudin kayan makaranta.
Wannan yana cikin matakan da gwamnatin baya ta dauka daf da za ta bar ofis, ko da sabuwar gwamnati ta zo, ba ta waiwayi karin kudin ba.
Jama'a su na wayyo Allah
A halin yanzu jama’a su na kokawa da yadda kudin karatun ya yi wani irin tashi daga N30, 000 zuwa N100, 000 daga watan Mayun 2023.
Amma duk da haka, ba a karbar kudin koyarwa a makarantun gwamnatin, masu kare gwamnati sun ce abubuwa ne su ka tashi a kasuwa.
Wani mai bibiyar shafin sada zumunta ya ce babu ta yadda za ayi a ajiye yaro a makarantar kwana na watanni, amma a biya masa N15, 000.
Radadin tallafin man fetur
Ma’aikata za su rika karbar N10, 000 a wata daga hannun Gwamnatin Kwara, rahoto ya zo cewa za a rika biyan kudin ne kafin ayi karin albashi.
Abdulrahman Abdulrazaq ya yi wa malaman lafiya karin alawus na musamman a jihar Kwara, kuma ya ce za a rabawa talaka abinci har gida.
Asali: Legit.ng