'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Boko Haram 4 Da Ake Zargin Sun Shirya Kai Hari Gidan Atiku Abubakar

'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Boko Haram 4 Da Ake Zargin Sun Shirya Kai Hari Gidan Atiku Abubakar

  • Jami'an tsaro sun damke wasu mutane hudu da ake zargin suna shirin kai hari gidan Atiku Abubakar
  • Mutane suna zargin wani dan Boko Haram ya je ya na tambayar gidan tsohon shugaban kasar a jiya Lahadi
  • Mai ba wa tsohon shugaban kasar shawara akan yada labarai ya tabbatar da kama mutanen hudu da suka shirya harin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Adamawa - Wasu da ke zargin na da hannu a shirin kai hari gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun shiga hannu.

Wadanda ake kaman su hudu ana zarginsu da shirya kai hari a gidan dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar PDP a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli.

'Yan sanda sun cafke 'yan Boko Haram da ake zargi da shirin kai wa Atiku hari
An Kama 'Yan Boko Haram 4 Da ke Shirin Kai Wa Tsohon Shugaban Kasa, Atiku Abubakar Hari. Hoto: Facebook.
Asali: UGC

Idan ba a mantaba, a jiya Lahadi 23 ga watan Yuli an kwamushe wani mutum da ya je ya na bincikar gidan tsohon shugaban kasar a birnin Yola da ke jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

Yadda aka kama dan Boko Haram da ake zargi shirya harin

Daga bisani aka damke shi a bakin mashigar gidan tsohon shugaban kasar tare da mika shi ga jami'an 'yan sanda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai ba wa Atiku Abubakar shawara a harkar yada labarai ya tabbatar da kama wadanda ake zargin a cikin wata sanarwa, Daily Nigerian ta tattaro.

Ya bayyana cewa bayan bincike mai zurfi daga jami'an 'yan sanda, mutumin ya bayyana sunansa da Jubrila Muhammad mai shekaru 29.

Jubrila ya kuma tabbatar da cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne daga karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno, cewar Daily Trust.

Ya ce akwai wasu wurare da suke son kai hari a Yola

A cewar sanarwar:

"Wanda ake zargin ya fadawa jami'an 'yan sanda cewa da shi da wasu 'yan uwansa da aka kama suna shirin kai hari kan wani kamfani na Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Babban Jagora a Kasar Yarabawa Ya Caccaki Tinubu Kan Wahalhalun Da Ake Sha a Najeriya

"Ya kuma ce akwai wasu wurare masu muhimmanci da suke son kai wa hari a cikin garin Yola.
"Dukkan wadanda ake zargin su hudu an mika su ga jami'an sojoji.

Tinubu Ya Shiga Matsi Bayan Sammacin Da Atiku Ya Yanko Masa A Amurka

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya shigar da bukatar soke sammacin da tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yanko masa.

Atiku Abubakar ya yanko sammancin ne daga kasar Amurka a wata kotu da ke Illinois cikin jihar Chicago.

Tsohon shugaban kasar na neman karin bayani na karatun Bola Tinubu daga jami'ar Chigaco.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.