Tsohon Sanatan PDP Ya Yi Babban Rashi, Matarsa Ta Rasu a Abuja

Tsohon Sanatan PDP Ya Yi Babban Rashi, Matarsa Ta Rasu a Abuja

  • Ɗan majalisa mai wakiltar jihar Abiya ta arewa a majalisar dattawa ta 8 ya yi rashin matarsa, Lady Nimi Ohuabunwa
  • Marigayya matar sanatan, wacce ta sha fama da jinyar wata cuta tsawon lokaci, ta mutu ne ranar Asabar, 22 ga watan Yuli a Asibitin Abuja
  • Sanata Ohuabunwa, tsohon shugaban majalisar ƙungiyar ECOWAS ne ya sanar da mutuwar mai ɗakinsa ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar mazaɓar Abiya ta Arewa, Sanata Mao Ohuabunwa, ya rasa mai ɗakinsa Lady Nimi Ohuabunwa.

Marigayya Lady Ohuabunwa, Lauya masaniyar doka a Najeriya ta rasu a wani Asbitin babban birnin tarayya Abuja, ranar Asabar 22 ga watan Yuli, 2023.

Sanata Ohuabunwa tare da marigayya matarsa.
Tsohon Sanatan PDP Ya Yi Babban Rashi, Matarsa Ta Rasu a Abuja Hoto: Senator Mao Ohuabunwa.
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa matar sanatan ta riga mu gidan gaskiya ne bayan fama da jinyar rashin lafiya ta tsawon lokaci a Asibiti.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Tsohuwar Kwamishiniya Ta Rasu a Jihar Kano

Matar Sanata Mao Ohuabunwa ta rasu

Tsohon sanatan karkashin inuwar jam'iyyar PDP da kansa ya sanar da rasuwar mai ɗakinsa a shafinsa na dandalin Facebook tare da wallafa Hotonta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da safiyar Litinin, 24 ga watan Yuli, 2023, Sanatan wanda ya wakilci Abiya ta arewa ya sanar da cewa:

"Cikin yanayin takaici tare da mika lamarin komai ga Allah mai girma, ina sanar da rasuwar masoyiyar matata kuma uwa ta gari ga 'ya'yana Ta rasu cikin ruwan sanyi ranar Asabar 22 ga watan Yuli."
"Muna buƙatar addu'arku a daidai wannan lokaci mai wahala da ƙunci ga iyalan gidanmu."

Tsohon gwamnan Abiya, Sanata Kalu, ya yi ta'aziyya

A halin yanzu, mazauna jihar Abiya da manyan jiga-jigan siyasa sun fara tura sakon ta'aziyyar rasuwar Lady Ohuabunwa.

Tsohon gwamnan Abiya kuma Sanata mai wakiltar Abiya ta arewa a majalisar dattawa ta 10, Sanata Orji Uzo Kalu ya nuna kaɗuwa bisa wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Koma Wa Abuja

Sanatan ya kuma ayyana rashin da, "Wani babban ciwo mai radaɗi da zai wahala a iya jure shi."

Rikici Ya Balle Tsakanin Manoma da Makiyaya a Jihar Kogi, Mutane da Dama Sun Mutu

A wani rahoton kuma Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da rikici ya ƙara balle wa tsakanin manoma da makiyaya a jihar Kogi.

Rikicin ya fara ne bayan wasu mahara sun mamayi manomi ɗaya a hanyarsa ta zuwa gona, sun halaka shi ranar Jumu'a. Bayan kwana biyu matasa suna kai harin ɗaukar fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262