Hukumar Alhazan Jihar Plateau Ta Musanta Batun Kisan Alhazai Tara a Mangu

Hukumar Alhazan Jihar Plateau Ta Musanta Batun Kisan Alhazai Tara a Mangu

  • Hukumar jindaɗin Alhazai ta jihar Plateau ta fito fili ta musanta batun kisan wasu Alhazai mutum tara bayan sun dawo daga Saudiyya
  • Rahotanni sun yaɗu cewa an halaka Alhazan ne akan hanyarsu ta komawa ƙauyukansu a ƙaramar hukumar Shendam
  • Sai dai, hukumar ta bayyana cewa labarin babu ƙamshin gaskiya a cikinsa domin dukkanin Alhazan jihar da suka dawo sun koma garuruwansu lafiya

Jihar Plateau - Hukumar jindaɗin Alhazan jihar Plateau ta musanta rahotannin dake yawo cewa an halaka Alhazai mutum tara akan titin hanyar Mangu-Shendam yayin komawa ƙauyukansu bayan sun dawo daga aikin Hajjin bana.

Rahotannin kisan Alhazan na zuwa ne a lokacin da ƙaramar hukumar Mangu ke fama da rikice-rikice inda mutane da dama suka halaka.

Babu Alhazan da aka kashe a Mangu
Hukumar Alhazan jihar Plateau ta musanta cewa an kashe Alhazai mutum tara a Mangu Hoto: @HaramainInfo
Asali: Twitter

A satin da ya gabata ne dai, labarin halaka Alhazan ya yaɗu a soshiyal midiya, lamarin da ya janyo mutane da dama suka yi ta yin Allah wadai da kisan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Tsohon Minista a Najeriya, Sun Tafka Barna

Menene abinda hukumar jindaɗin Alhazan tace dangane da lamarin?

Namu Sanusi, kakakin hukumar jindaɗin Alhazan ta jihar ya gayawa jaridar Daily Trust cewa dukkanin Alhazan jihar mutum 1,500 sun dawo lafiya daga ƙasa mai tsarki sannan dukkaninsu sun koma garuruwansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Na kira mutane da dama a yankunan da aka ce an halaka Alhazai, amma babu wanda ya ce min an halaka wani mahajjaci akan hanyarsu bayan sun dawo daga Jos."
"Abinda kawai muka sani shi ne daga cikin Alhazai 1,500 da suka je aikin Hajji daga jihar Plateau, mutum biyu sun rasu a Saudiyya. Bayan wannan babu wanda ya rasu. Mun gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan ba wanda aka kashe."

Kakakin hukumar ya yi kira ga jama'a da su yi fatali da labarin kisan Alhazan, rahoton Trust Radio ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Daliban Sakandare Sun Lakada Wa Malami Dukan Tsiya Saboda Ya Hana Su Satar Amsa A Ogun

Babban Limami Ya Rasu Bayan Ya Dawo Daga Saudiyya

A wani labarin kuma, babban limamin babban masallacin Suleja dake a jihar Neja ya riga mu gidan gaskiya sa'o'i kaɗan bayan ya dawo daga Saudiyya.

Sheikh Dahiru Shuaibu ya koma ga mahaliccinsa yana da shekara 76 a duniya inda ya bar matam aure guda huɗu, ƴaƴa 30 da jikoki da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng