Lambar Ministan Buhari Ta Fito, Gwamnatin Tinubu Za Ta Bincike Shi Kan Abubuwa 5
- Gwamnatin Najeriya za tayi bincike a kan Abubakar Malami wanda ya rike AGF daga 2015 zuwa 2023
- Tsohon Ministan zai amsa tambaya a kan kudin da gwamnatin tarayya ta biya lauyoyi da kamfanoni
- Abubakar Malami SAN yana cikin Ministocin da su ke da karfi a mulkin Muhammadu Buhari
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja- Akwai wasu ciniki da yarjejeniya da aka shiga a lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki da su ka jefa Abubakar Malami a matsala.
Wani rahoto na musamman da aka samu daga The Cable ya nuna cewa akwai zargin badakala akalla biyar da ke wuyan Abubakar Malami SAN.
Daga ciki akwai Dala miliyan $496 da kamfanin Global Steel Holdings Ltd (GSHL) ya biya gwamnatin tarayya kan kwangilar kamfanin Ajaokuta.
Binciken EFCC da Paris Club
Tsohon Ministan shari’an kasar zai amsa tambayoyin inda aka kai kadarori da sauran kudin da EFCC ta karbe daga hannun marasa gaskiya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Baya ga haka, za a ji gaskiyar dalilin biyan Dala miliyan $419 ga wasu kwararru daga kudin Paris Club, a yayin da Malami yake rike da ofishin AGF.
Binciken ya tabo Dala miliyan $200 da gwamnatin Najeriya ta biya kamfanin Sunrise Power sakamakon sabanin da aka samu a aikin wutan Mambilla.
Ana zargin an biya kudin shari’a sau biyu domin karbo Dala miliyan $321 da aka karbe daga hannun Marigayi Janar Sani Abacha a Switzerland.
A lokacin Kayode Fayemi yana Minista, ya ce an shawo kan matsalolin kamfanin Ajaokuta, daga baya aka ji Malami ya ce za a biya $496m ga GSHL.
Rahoton ya ce ana zargin Malami ya ba EFCC ta ofishin Ladidi Mohammed umarnin yin gwanjon wasu kadarori da hukumar ta yi nasarar karbewa a kasar.
Wajen aikin wutan Mambila, tsohon Lauyan da Saleh Mamman su ka sa hannu aka biya kamfanin SPTCL dalolin kudi domin su janye kararsu a kotu.
A kokarin dawo da kudin Abacha daga Switzerland, gwamnatin tarayya ta biya $17m ga wasu lauyoyi, wannan yana cikin dalilin binciken tsohon Minista.
Bashin Paris Club ya jawo rikici
A baya an ji labari NGF ta sa kafar wando daya da Abubakar Malami kan bashin Paris Club saboda ya ce za a biya kudi ga wasu da sunan kudin aiki.
Malami ya zaftare fiye da N170bn daga asusun jihohi da kananan hukumomi a 2022, ya ce zai biya wasu da su ka taimaka har aka iya dawo da dalolin.
Asali: Legit.ng