Tashin Hankali Yayin da Wata Sabuwar Kwayar Cuta Ta Bullo, Tana Kama Kubewar Miya
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu bullar wata kwayar cuta a gonakin kubewa a fadin kasar nan
- An samu labarin cewa, kwayar cutar na kama amfanin gona, musamman kubewa da manoma ke nomawa a wannan shekarar
- Ya zuwa yanzu, majiya ta bayyana abubuwan da hukumomi ke yi don ganin an samu hanyar dakile yaduwar wannan kwayar cuta
Najeriya - Cibiyar Nazarin Kayan Lambu ta Kasa (NIHORT) ta gano wata kwayar cuta da ke addabar lafiyar gonakin kubewa a Najeriya.
Hukumar gudanarwar NIHORT ta ce manoman da ke samarwa ‘yan Najeriya kubewa sun koka kan yadda kwayar cutar ke lalata musu dukiya a kusan 70% na dukkan gonakinsu.
Hukumar ta ce, ta samu rahoton bullar kwayar cutar ne daga jihohin Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Ekiti, Legas da Neja, Aminiya ta ruwaito.
Hakazalika, ta kuma ce bayan da jami’anta suka gudanar da bincike mai zurfi, sun gano cewa kwayar cutar ce ta haifar da matsala a gonakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda cutar ta ke a zahirinta
NIHORT ta ce alamomin kwayar cutar sun hada da bayyanar wani dunkule kullutu a karkashin ganyen kubewar, inda daga baya kuma ganyen zai lankwashe ya koma launin rawaya.
A bangarenta, NIHORT ta shawarci manoma da su ci gaba da amfani da magungunan feshin kwari a duk mako da zarar sun ga alamun bullar kwatar cutar a gonakinsu.
Matakin da ake dauka a yanzu
Kuma hukumar ta ce tana aiki tukuru ba dare ba rana domin nemo maganin da zai kashe kwayar cutar nan take kowa ma huta, Tribune Online ta ruwaito.
Ana yawan samun bullar cututtuka da ke addabar dabbobi ko kayayyakin shuka a Najeriya, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata.
Lamari ya gwabe a Arewa, Musulmai da Kirista sun yi sallar rokon ruwa a wata jihar Arewa
A bangare guda, Musulmi da Kirista sun gudanar da addu’o’in rokon samun ruwan sama da kuma ci gaban zaman lafiya a jihar Borno.
Jama’a da dama ne suka taru a Maiduguri babban birnin jihar domin yin addu’ar rokon ruwan sama a yayin da ake fama da fari a sassan jihar.
An ruwaito cewa, an yi sallar rokon ruwa a masallatan Juma'a da dama a jihar, kana aka gudanar addu'o'i a cocin Baptist da birnin Maiduguri a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng