Gwamnatin Jihar Ebonyi Ta Sha Alwashin Raba Kayan Tallafin Ga Al'ummar Jihar

Gwamnatin Jihar Ebonyi Ta Sha Alwashin Raba Kayan Tallafin Ga Al'ummar Jihar

  • Gwamatin jihar Ebonyi ta shirya faranta ran al'ummar jihar a yayin da ke cikin halin matsi a dalilin cire tallafin man fetur
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa tana shirin rabawa al'ummar jihar kayan tallafi domin rage musu raɗaɗi
  • Sai dai, gwamnatin tace za ta yi rabon ne bayan ta ga kamun ludayin rabon kayan tallafin da gwamnatin tarayya za ta yi wa ƴan Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ebonyi - Gwamnatin jihar Ebonyi ta bayyana cewa tana sane da halin matsin tattalin arziƙin da al'ummar jihar ke ciki kan cire tallafin man fetur, sannan ta sha alwashin kawo hanyoyin da za su rage musu raɗaɗi.

Gwamnatin ta bayyana cewa tana duba kan yanayin tallafin da gwamnatin tarayya za ta ba ƴan Najeriya domin samar da irinsa bisa daidai ƙarfinta ga al'ummar jihar Ebonyi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

Gwamnatin jihar Ebonyi za ta raba kayan tallafi
Gwamnatin jihar Ebonyi za ta faranta ran al'ummar jihar Hoto: @Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Kwamishinan watsa labarai da wayar da kai na jihar, Jude Okpor, shi ne ya bayyana haka a yayin wani taro da ƴan jarida a birnin Abakaliki, ranar Lahadi, 23 ga watan Yulin 2023.

Gwamnatin ta fara da yi wa ma'aikata ƙarin albashi

A cewarsa ƙarin albashin ma'aikata da gwamna Nwifiru ya yi, na daga cikin hanyoyin da gwamnatin jihar ke bi wajen rage raɗaɗin da al'ummar jihar ke sha.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Ruwa daga sama yake faɗowa zuwa ƙasa. Jihar Ebonyi za ta jira saboda tana ayyukanta ne tare da gwamnatin tarayya. Za mu jira mu gani menene gwamnatin sama za ta yi dangane da tallafi, daga nan sai mu zauna mu duba mu gani abinda mu ke da shi zai yi daidai da hukuncin da za mu yanke."
"Ba za mu yi gaggawar ɗaukar wani mataki ba dangane da wannan lamarin. Hakan ya sanya mai girma gwamna ya yi hikimar rage raɗaɗin ma'aikatan jihar Ebonyi ta hanyar ƙara musu albashi.

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

"Muna sane da cewa gwamnatin tarayya a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu tana shirin yin rabon kayan tallafi ga ƴan Najeriya domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur. Al'ummar jihar Ebonyi su ma za su amfana da wannan tallafin."

NEC Ta Yi Bayani Kan Tsarin Rabon Tallafi

A wani labarin kuma, majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) ta cimma matsaya yadda za a raba tallafin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Majalisar ta bayyana cewa kowace jiha ita ce da kanta za ta raba tallafin kuɗin da shugaba Tinubu zai bayar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng