Tsumagiyar Tallafin Fetur Ta Bugi Gwamnoni, Ana Tunanin Rage Facakar Kudi
- Charles Chukwuma Soludo ya yi bayanin abin da Gwamnoni su ka tattauna a taron NEC a Aso Rock
- Gwamnan yana ganin bai dace a matsawa talakan Najeriya, kuma a bar masu mulki su na bushasha ba
- Soludo ya bada misalin yadda aka rage barnar kudin da ake yi da ya karbi mulkin Jihar Anambra a 2022
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Gwamna Charles Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya ce masu mulki sun fara duban kan su bayan janye tallafin fetur a Najeriya.
The Cable ta ce Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan bayani a karshen taron majalisar NEC da aka yi a karshen makon da ya gabata.
Gwamnan na jihar Anambra ya ce rashin tausayi ne gwamnonin jihohi su rika yawo da tawagar motoci kusan 20 a irin halin da ake ciki a yau.
Maganar Charles Chukwuma Soludo
"Wannan abu ne da ya sha bam-bam, ba lamari ne da za a zauna a taro ayi wa kowace jiha doka ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Amma tun da majalisar (NEC) ta lura da wannan, abin dumuwa ne da kowane bangaren gwamnati ya kamata ta duba a matsayin matsalarta.
Dole mu canza yadda ake tafiyar da jihohi, wani ya bada misalin yadda wani gwamnan jiha yake yawo da motoci 20, duk ana sa masu mai."
- Charles Soludo
An rahoto Farfesa Soludo yana cewa NEC tayi masu bayanin bukatar tsuke bakin aljihu, su ma su yi irin hakurin da ake fadawa talakawa su yi.
Misali da Gwamnatin Jihar Anambra
"Lokacin da na shiga ofis, alal misali, ana kashe N137m wajen share ofisoshin gwamnati, a yau a Anambra N11m mu ke kashewa kan shara.
Wannan abu ne da mu ke so kowane cikinmu ya duba, mu duba kudin da mu ke kashewa."
- Charles Soludo
Tsohon Gwamnan babban bankin kasar yake cewa babu ruwan majalisar NEC da inda kudin jihoh yake tafiya, illa iyaka a ba abokan aikinsa shawara.
Tashin Dala ne hadarin - Masani
An samu labari Dr. Usman Adamu Bello wanda masani ne kan tattalin arziki, ya ce hadarin tashin Dala ya fi na tsadar man fetur da ake kuka da shi a yau.
Malamin jami'ar ya ce Bola Tinubu ya yi garajen karya Naira da janye tsarin tallafin fetur ba tare da ya yi zama da kwararru domin a duba tasirin hakan ba.
Asali: Legit.ng