'Yan Bindiga A Zamfara Sun Yi Barazanar Auren 'Yan Mata 4 Da Ke Hannunsu
- Masu garkuwa da mutane sun yi barazanar auren wasu 'yan mata hudu nan da mako daya idan ba a biya kudi ba
- An kama 'yan matan ne akan hanyar Birnin Magaji zuwa Kaura Namoda watanni shida da suka wuce
- Iyalan 'yan matan su hudu sun roki gwamnati da al'umma da su kawo musu dauki don ceto yaran
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi barazanar auren 'yan matan da suka yi garkuwa da su idan iyayensu suka gagara biyan kudin fansa.
'Yan bindigan sun sace 'yan matan ne su hudu akan hanyar Birnin Magaji zuwa Kaura Namoda da ya hada da wata dalibar Kwalejin Kimiyya da Adabi ta jihar inda suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 12.
'Yan matan da aka kaman watanni shida da suka wuce sun bayyana yadda 'yan bindigan suke musu barazanar aure a wani faifan bidiyo, cewar gidan talabijin na Channels.
Matan sun hada da Ummukhair da Aisha Yahaya da Jemila Yahaya sai kuma Ummu Sani.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sun ce tsagerun sun ba wa iyayensu mako daya su kawo kudin fansa ko kuma su aure su gaba daya, cewar Ripples.
A cewarsu:
"Muna rokonku iyayen mu don girman Allah, muna cikin wani hali, don Allah ku nemo kudi don samar mana 'yanci.
"Gwamnatin Matawalle ta gaza yin wani abu, wannan watan mu na shida kenan, muna rokon Dauda Lawal ya yi wani abu."
Daya daga cikin 'yan uwan matan da aka kaman, Aminu Yahaya ya bayyana cewa su shida aka kama amma an saki biyu bayan biyan kudin fansa na N6m, Daily Post ta tattaro.
"Ni na kai kudin fansa N6m kafin suka saki 'yan mata biyu.
"Yanzu sun bamu mako daya idan ba mu kawo N12m ba za su auri kannenmu."
Ya roki gwamnati da kuma al'umma da su kawo musu dauki.
Rundunar Soji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga Da Dama a Jihar Zamfara
A wani labarin, rundunar soji sun hallaka wasu 'yan bindiga da dama a jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar cewa sojojin sun hallaka 'yan bindigan bayan kai samame maboyar 'yan ta'addan.
Ƙauyukan da sojojin suka kai hari akwai Mutuwa da Guda Tudu da Kawar da kuma Dan Kare da ke jihohin Zamfara da Sokoto.
Asali: Legit.ng