'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu Da Sace Wasu Mutum Biyu a Jihar Bauchi

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyu Da Sace Wasu Mutum Biyu a Jihar Bauchi

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi a yankin Arewa maso Gabas
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum biyu tare da yin awon gaba da wasu mutum biyu daban
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun aike da saƙo wajen waɗanda aka sace ɗin da su tanadar musu N10m

Jihar Bauchi - Wasu ƴan bindiga sun halaka mutum biyu a wani farmaki da suka kai a ƙauyen Tamba cikin ƙaramar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Mazauna yankin sun gayawa jaridar Premium Times cewa jami'an tsaro da ƴan sakai sun garzaya wajen da gaggawa inda suka kai mutum biyun zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Yan bindiga sun halaka mutum biyu a Bauchi
'Yan bindiga sun halaka mutum biyu da sace wasu mutum biyu a jihar Bauchi Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Haka kuma ƴan bindigan sun sace wasu mutum biyu a ƙauyen Kafin Lemo cikin ƙaramar hukumar ta Ningi a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Sace 'Ya'yan Wani Babban Dan Siyasa a Najeriya, Sun Nemi Kudin Fansa Na Makudan Kudi

Ƴan bindigan sun nemi da a tanadar musu kuɗi kafin su zo

A cewar mazauna yankin waɗanda aka sace ɗin su ne Yawale Lemo mai shekara 55 a duniya da Kwaine Musa mai shekara 50 a duniya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani majiya wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa:

"Mutum biyu mazauna ƙauyen nan, Kafin Lemo, ƴan bindiga sun sace su bayan sun shigo ƙauyen da misalin ƙarfe 2:00 na dare."
"Ƴan bindigan sun kira mutum biyun kan cewa su tanadar musu N10m kafin su zo. Rashin tanadar musu kuɗin shi ne dalilin da ya sanya suka kawo harin."
"Har ya zuwa yanzu ƴan bindigan basu kira iyalansu ba domin sanar musu a inda suke ko yawan kuɗin da za su kawo a matsayin kuɗin fansa kafin a sake su."

Majiyoyi sun bayyana cewa tawagar ƴan sanda da ƴan sakai sun shiga cikin dajin dake yankin neman mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Al'ummar Bauchi Sun Zargi Sarakuna Da Kwace Musu Fili

A wani labarin kuma, al'ummar ƙauyen Tulu na yankin Lame a ƙaramar hukumsr Toro ta jihar Bauchi sun koka kan ƙwacen filin da ake yi musu.

Mutanen yankin dai suna zargin mai unguwar Tulu da haɗa baki da wasu suna ƙwace musu gonaki da filaye ana cefanar da su a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng