Dalibai Sun Yi Wa Malaminsu Dukan Tsiya Bayan Ya Hana Su Satar Amsa
- Jami'an 'yan sandan jihar Ogun sun kama wasu matasa dalibai da ake zargin sun daka malaminsu a makaranta
- Daliban su goma ana zarginsu da cin zarafin malamin bayan ya kama daya daga cikinsu ya na satar amsa
- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Omotola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an kwamushe daliban
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Gungun wasu dalibai sun ci zarafin malaminsu mai suna Kolawale Shonuga kan hana daya daga cikinsu satar amsa.
Daliban su 10 sun ci zarafin malamin ne a ranar Talata 18 ga watan Yuli a makarantar Isanbi Comprehensive a karamar hukumar Ikenne da ke jihar.
Malamin ya sha duka bayan hana daliban satar amsa
Malamin ya kama daya daga cikinsu Ashimi Adebanjo mai shekaru 18 yayin kula da jarabawar a makarantar inda ya kwace tare da yaga takardarsa.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan an tashi a makaranta, daliban sun tare malamin a bakin mashigar makarantar tare da masa duka, Daily Trust ta tattaro.
Daya daga cikin daliban, Kazeem Adelaja ya buga masa sanda a kai yayin da sauran suka ci gaba da dukansa.
'Yan sanda sun cafke daliban
'Yan sandan yanki da ke ofishin Remo sun kawo samame wurin da abin ya faru tare da kama 10 daga cikin daliban, cewar Premium Times.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Omotola Odutola ta ce malamin ya kai rahoton abin da ya faru a ofishin yanki na Remo.
Rahotanni sun tabbatar da tura yaran zuwa kotu don daukar mataki amma mai hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda bai yi bayani a kan kama daliban ba.
Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da irin wanna aika-aika inda ta ce ba za ta bari irin wannan rashin tarbiya na faruwa a jihar ba.
Mai ba wa gwamnan jihar shawara akan harkan ilimi, Farfesa Abayemi Arigbabu shi ya bayyana haka a birnin Abeokuta.
'Yan Sanda Sun Kwamushe Wasu Da Ake Zargi Da Satar Mahaifa A Ogun
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wasu ma'aikatan jinya bisa zargin satar mahaifa.
Ana zargin ma'aikantan ne da ke aiki a cibiyar lafiya ta Comprehensive da ke Owo a jihar.
Daga cikin wadanda aka kaman akwai wani mai gadi da suka hada baki don aika-aikar.
Asali: Legit.ng