Katsina: Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Matashi Yayin Garkuwa Da Wani Yaro

Katsina: Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Matashi Yayin Garkuwa Da Wani Yaro

  • Tsagera 'yan bindiga sun yi ajalin wani matashi a karamar hukumar Kankia da ke jihar Katsina
  • Marigayin mai suna Ibrahim Abdullahi ya rasa ransa ne bayan kawo ziyara ga dan uwansa
  • Dan uwan mamacin ya bayyana yadda abin ya faru inda ya ce 'yan bindigan sun sake yaron da suka sace da farko

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun hallaka wani matashi a garin Kankia hedkwatar karamar hukumar Kankia da ke jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 22 ga watan Yuli a garin Kankia kusa da babban asibiti lokacin da marigayin ya kai ziyara ga dan uwansa.

Tsageru 'Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Matashi Yayin Garkuwa Da Wani Yaro A Katsina
Jihar Katsina Na Fama Da Hare-Haren 'Yan Bindiga. Hoto: Dailly Trust.
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindigan suka hallaka matashin

Marigayin mai suna Ibrahim Abdullahi da aka fi sani da Baraya ya na tsaye da misalin karfe 9 na dare a bakin kofar gidan kawai ya ji harbi ya same shi, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin 'yan uwansa mai suna Muhammad ya ce sun yi tsammanin jami'an tsaro ne bayan da suka ji harbin bindiga.

A cewarsa:

"Muna cikin harkokinmu sai muka ji karar bindiga, mun so mu gudu sai muka yi tsammanin jami'an tsaro ne tun da ba mu sake jin karar bindigar ba.
"Daga baya muka fahimci Ibrahim wanda dan uwa ne a gun matana, an dauke shi zuwa asibiti mafi kusa, yanzu haka gawarsa na asibitin.

Katsina na fama da hare-haren 'yan bindiga

Ya kara da cewa 'yan bindigan da farko sun sace wani yaro, amma bayan harbin bindigan sun sake shi suka tsere, cewar TheCable.

Jihar Katsina na fama da hare-haren'yan bindigan da suka addabi mutane musamman na karkara.

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a yankunan tun baya nada sabbin hafsoshin tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Babban Jagora a Kasar Yarabawa Ya Caccaki Tinubu Kan Wahalhalun Da Ake Sha a Najeriya

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda Ta Sama, Sun Hallaka Mayaka Da Dama A Katsina

A wani labarin, sojoji sun kashe mayaka da dama a jihar a Katsina wadanda suka addabi jama'ar jihar.

Sojojin sun musu lufguden wuta ne ta sama da kasa a yayin wata samme da suka kai a maboyar 'yan bindigan a kananan hukumomin Batsari da Jibia.

Mafi yawa daga cikin 'yan bindigan na biyayya ga Abdulkarim Boss, wani kasurgumin dan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.