An Sha Biki, Buhari Ya Halarci Daurin Auren Dan Gwamnan Borno, Hotuna Sun Yadu
- An daura auren dan gidan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da amaryarsa a birnin Maiduguri
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu halartar bikin tare da wasu manyan jiga-jigan kasar nan
- Wannan ne karon farko da Buhari ya halarci wani biki a cikin gida Najeriya tun bayan saukansa a mulki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Maiduguri, Borno - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren dan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.
A hotunan da gidan talabijin na kasa (NTA) ya yada, an ga lokacin da tsohon shugaban ke zaune tare da wasu manyan jiga-jigan kasar nan.
A cewar rahoton, bikin ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu manyan bakin da suka fito daga bangarori daban-daban na kasar nan.
Buhari da Shettima ne suka jargoranci daurin auren
Hakazalika, rahoton ya bayyana cewa, tsohon shugaba Buhari ne da Kashim Shettima suka jagorancin dauren auren amarya da angon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan gwamna Zulum, Muhammad Babagana ya angwance ne da amaryarsa Ummi Khaltum a birnin Maiduguri a jihar ta Borno.
Wani bangare na sanarwar da NTA ta yada tare da hotunan jiga-jigan kasar nan a wurin daurin auren ya ce:
“Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka jagoranci daurin aure tsakanin Muhammad Babagana Umara Zulum da Ummi Khaltum tare da manyan baki a fadin kasar nan.
“Sun hada da gwamnonin jahohi 11, mataimakan gwamnoni, ‘yan majalisun kasa da na Jihohi, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da dai sauransu.”
Wannan ne karon farko da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani biki a cikin gida Najeriya tun bayan saukan a mulkin kasar nan.
Tafiyar farko zuwa kasar waje da shugabannin Najeriya suka yi tun daga 1999
A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa kasar Faransa bayan kwanaki 23 da hawa kan karagar mulkin kasar nan.
Shugaban kasar zai halarci wani taro ne a ƙasar kan tattalin arziƙi wanda zai gudana a ranakun 22 da 23 na watan Yunin 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasar kan ayyuka na musamman da watsa labarai, Dele Alake, ya fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Yunin 2023.
Asali: Legit.ng