Daga Karshe Majalisar Dattawa Tayi Magana Akan Wadanda Tinubu Zai Nada Su Zama Ministocinsa
- Jinkirin da shugaba Bola Tinubu ya yi na aika sunayen ministocinsa zuwa majalisar dattawa zai tilastawa majalisar dakatar da hutun da take yi na shekara-shekara
- A ranar 27 ga watan Mayu ne ake sa ran majalisar dattijai za ta fara hutun ta, sai dai wata majiya daga majalisar ta bayyana cewa ana sa ran ganin jerin ministocin daga farkon mako mai zuwa
- Sai dai kakakin majalisar dattawan ya ce ba a bayyana ranar hutun ba, kuma babu bukatar a yi muhawara kan karin wa'adin tafiya hutun
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Majalisar dattawa za ta dakatar da hutun da za ta yi na shekara saboda an ce tana sa ran ganin ministocin da shugaba Bola Tinubu ya nada domin tantance su.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, 'yan majalisar na jiran jerin sunayen ne daga fadar shugaban kasa a farkon mako mai zuwa.
Wani babban jami’in majalisar dattawan ya bayyana cewa ana sa ran majalisar ta fara hutun shekara-shekara, wanda ake sa ran zai fara daga ranar 27 ga watan Yuli zuwa Satumba.
Dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta dakatar da hutun shekara
Sai dai, yanzu an ce majalisa a shirye take ta rika zama a kowace rana domin tabbatar da an tantance wadanda Tinubu zai nada, koda kuwa hakan na nufin za a daga lokacin tafiya hutun da mako guda.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yada labarai, Yemi Adaramodu, ya ce majalisar na da karin lokaci don duba bukatar shugaban kasa kafin a tafi hutu.
A cewarsa, har yanzu ba a bayyana ranar da za a fara hutun shekaran ba. Don haka, tambayar canjin lokacin ma bai taso ba.
Majalisar dattawa za ta duba jerin sunayen ministocin shugaba Tinubu
Yace:
"Har yanzu akwai isasshen lokaci na gudanar da tantance sunayen ministocin."
Adaramodu ya ci gaba da cewa, majalisar dokokin kasar za ta yi abin da ya dace kuma ‘yan Najeriya ba za su ji kunya ba.
A baya dai an ruwaito cewa shugaba Tinubu ya mika sunayen wadanda aka nada a matsayin ministoci ga majalisar dokokin kasar.
An kuma bayyana cewa shugaban ya aika da jerin sunayen ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) domin tantancewa.
Jerin mutane 50 da Bola Tinubu ya fito da su a siyasa har Duniya ta san da zamansu yau
A wani jeri da yake yawo a kafafen sada zumunta, Legit.ng Hausa ta tattaro sunayen wasu da-dama daga cikin wadanda za a kira yaran Bola Tinubu.
A baya, mun tuntubi Hadimin Gwamnan jihar Legas, Jibril Gawat domin jin yadda lamarin yake.
Jibril Gawat ya shaida mana cewa gwanin na su ya kafa mutanen da ba za su kirgu ba, ya kuma yi alkawarin zai tattaro mana sunayen wasu daga cikinsu.
Asali: Legit.ng