Ana Tsaka da Tsadar Kayayyaki, Kwastam Ta Kwace Shinkafa, Taliya da Man Gyadan da Aka Shigo da Su Najeriya

Ana Tsaka da Tsadar Kayayyaki, Kwastam Ta Kwace Shinkafa, Taliya da Man Gyadan da Aka Shigo da Su Najeriya

  • Hukumar Kwastam ta Najeriya ta samu nasarar kama kayayyaki 179 da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1 a watan Mayu da Yulin bana
  • A cewar jami’an hukumar ta kwastam, an kwato haramtattun kayayyakin ne a wurare da dama a fadin kasar nan
  • Kayayyakin sun hada da shinkafar waje da kayan sawa gwanjo, sabulun waje, man gyadan waje, taliya da ababen hawa

Sashin tarayya na hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (NCS) da ke shiyyar B a Kaduna, ta kama kayan abinci, motoci da sauran haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1 tsakanin watan Mayu zuwa Yulin bana.

Hakan na zuwa ne bayan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai 22.7% wanda hakan ya sa kasar ta fi kowacce kasa karfin sayen kayan waje a Afirka, kamar yadda majiyar Legit.ng ta fada.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Na Kan Gaba a Yawan Wadanda Suka Kamu Da Cutar Mashako a Najeriya

A wani rahoton jaridar Punch, an ce jami’in hulda da jama’a na rundunar, Isah Sulieman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce a cikin lokacin da hukumar ta yi aikin, ta kama kayayyaki sau 179.

Yadda aka kama kayan kasar waje a Kaduna
Kayayyakin da Kwastam ke kwatowa | Hoto: NAN
Asali: UGC

Jumillar kamu 179 da aka yi

A cewar shugaban hukumar kwastam mai kula da sashin, Musa Jalo, an kwato haramtattun kayayyakin ne a wurare da dama a fadin yankin na Arewa maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jalo ya ce rundunar ta samu damar yin jimillar kame 179 na kayayyakin da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 1 a wurare daban-daban a shiyyar musamman ta hanyar leken asiri da bin kwakwaf.

Ya kara da cewa kayayyakin da aka kama sun yiwu ne tare da taimakon rundunar hadin gwiwar jami’an sintiri na hukumar a kan iyakokin jihar Kebbi, Neptune Prime ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: “Rabon N8,000 Duk Yaudara Ce”, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili

Ya zayyana wasu daga cikin kayayyakin da da aka kaman kamar su shinkafar waje da kayan sawa gwanjo, sabulun waje, man gyadan waje, taliya da ababen hawa.

Jerin abubuwan da Hukumar Kwastam ta kama

  1. Tsoffin mooci 21 da aka shigo dasu da kuma 11 na ‘yan rakiya
  2. Buhu 2234 na shinkafa ‘yar waje kowacce mai nauyin kilogiram 50, da kuma 48 mai nauyin kilogiram 25
  3. Jarakuna 226 na man gyadan waje mai lita 25 kowanne
  4. Katan 2,780 na taliya, macaroni, da kuskus,
  5. Dauri 278 na gwanjon sutura, buhu 15 na takalmi gwanjo dan waje,
  6. Katan 140 na gwangwanayen tumatir dan waje da man shafawa dan waje,
  7. Madara mai kauri ‘yar waje,
  8. Koren shayin dan waje,
  9. Madaran gari ‘yar waje,
  10. Katan 149 na ruwan 'ya'yan itace dan waje,
  11. Sabulun waje,
  12. Ashana ‘yar waje,
  13. Jarakuna 140 na gas din motoci mai yawan lita 25 kowanne,
  14. Jarakuna 140 na man fetur mai yawan lita 25 kowanne

Kara karanta wannan

Ya shafi kowa: Yadda 'yan damfara suka wawuri kudade N1bn da asusun bankin 'yan Najeriya

Yadda 'yan damfara suka wawuri kudade N1bn da asusun bankin 'yan Najeriya

A wani labarin, kusan Naira Biliyan 1 ne aka yi hasararsu ta dalilin zamba da sata ta hanyoyin biyan kudi da mu'amalar yau da kullum a cikin kwata na farko na 2023.

Hakan ya biyo bayan fargabar da Hukumar Inshorar Ajiyar Kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana kan yawaitar satar da ake samu a bankuna.

An bayyana hakan ne a cikin wani rahoto mai suna, "Rahotanni kan zamba da sata a bankunan Najeriya", wanda cibiyar horar da harkokin kudi (FITC) ta buga kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.