Ta Kare Wa ’Yan Awaren IPOB Yayin da Sojoji da DSS Suka Taru, Suka Musu Fatattakar Kare
- Rundunar sojin Najeriya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS)a gamayar hadin gwiwa sun yi nasarar murkushe mayakan ‘yan ta’addan IPOB
- An tattaro cewa sojojin Najeriya da mayakan na IPOB sun gwabza kazamin artabu a yayin farmakin da aka kai
- Rahotanni sun ce sojojin sun kama wasu daga cikin mayakan na IPOB, inda suka kuma kwace muggan bindigogi da alburusai
Delta, Asaba - A yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula da masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da kuma sojojinsu na ESN ke haddasawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, rundunar sojojin Najeriya ta bankado wata maboyarsu a garin Asaba da ke jihar Delta.
A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta bayyana cewa dakarun 63 Bde Garrison da ke karkashin runduna ta 6, tare da hadin gwiwar jami’an DSS sun kai wani samame kan wadannan ‘yan ta’addan.
A cewar sanarwar, sojojin Najeriya sun yi wa daya daga cikin maboyar IPOB/ESN kwanton bauna a jihar Delta a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli.
Sanarwar ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Rundunar sojin ta gudanar da wani samame a kan wata maboyar ‘yan ta’addan da ke tsakiyar wani babban dajin da sanyin safiya.
“Sojojin sun samu galaba a kan mayakan IPOB a musayar wuta da suka yi biyo bayan arangamar, lamarin da ya tilasta musu barin maboyar cikin tashin hankali."
Sojoji, IPOB sun gwabza fada
An tattaro cewa yayin musayar wuta tsakanin ‘yan tawayen na IPOB da jaruman sojojin Najeriya, an kama daya daga cikin mayakan na IPOB.
Hakazalika, an kwato wasu bindigogi da alburusai daga matsugunin 'yan tawayen na IPOB da ke dajin na Delta.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Sojojin sun kama daya daga cikin mayakan da suka tsere tare da kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyar, PASAR guda uku, G3 daya da kuma bindigar mai ganga guda daya.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
“Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da alburusai, zarto mai aiki da wutar lantarki, adduna, gatari da tutar IPOB.
"Sojojin sun lalata maboyar tare da yin gangami a cikin dajin wajen fatattakar mayakan da suka tsere."
Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya yabawa sojojin da sauran jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na gudanar da ayyukanSU, ya kuma bukace su da su ci gaba da zage damtse don dawo da hayyaci yankin.
An kama shugaban Inyamurai da ya yi barazanar kai 'yan IPOB Lagas
A wani labarin na daban, an kama Fredrick Nwajagu, shugaban 'yan kabilar Igbo da ya yi barazanar tattaro 'yan ta'addan IPOB ya kawo Legas.
A cikin wani bidiyo, an ga yana barazanar gayyatan mambobin haramtaciyyar Kungiyar IPOB zuwa Lagas da sunan kare kadarorin yan kudu maso gabas, jaridar Punch ta rahoto.
Kungiyar IPOB dai wata kungiya ce ta 'yan ta'addan da ke kokarin ballewa daga Najeriya saboda wasu dalilai.
Asali: Legit.ng