“Ban Yarda Da Sallamawa Miji Albashi Ba”: Wata Mata Ta Magantu a Gaban Mijinta

“Ban Yarda Da Sallamawa Miji Albashi Ba”: Wata Mata Ta Magantu a Gaban Mijinta

  • Wata mata mai wayo, Bukola Ipinyomi, ta yi watsi da matan auren da ke mikawa mazajensu albashinsu sannan su dunga basu kadan-kadan
  • Bukola ta bayyana cewa ita da mijinta suna hada hannu wajen kula da gidan sannan basu taba bude asusun ajiya na hadin gwiwa ba
  • Matar ta bayyana cewa ta fi mijin iya maleji idan aka zo kan maganar kudi domin shi yana iya kashe kudi ba tare da ya yi tsare-tsare ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mata, Bukola Ipinyomi, ta magantu kan yadda take samun kudi fiye da mijinta a lokacin da suka yi aure.

Matar ta bayyana cewa ba za ta iya mikawa mijinta albashinta ba saboda baya duba yadda yake kashe kudi.

Matar aure ta ce ta fi mijinta lura da yadda take kashe kudi
“Ban Yarda Da Sallamawa Miji Albashi Ba”: Wata Mata Ta Magantu a Gaban Mijinta Hoto: @sojiolayinka_rt
Asali: TikTok

Matar ta kara da cewar tana samun kudi fiye da shi a lokacin da suka yi aure. Ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

"Ba za mu iya bude bankin hadin gwiwa ba saboda na fi mijina iya maleji idan aka zo maganar kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bukola ta bayyana cewa kafin ta yi aure, ta riga ta saka a ranata cewa za ta auri mijin da ya shirya yin aiki ne kawai don su hada hannu tare.

Ta ga laifin mata da ke mikawa mazajensu albashinsu sannan su koma dogaro da su don siyan abubuwa kamar su kayan kamfai. @sojiolayinka_rt ne ya wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Atakiti Micheal ya ce:

"Kalli yadda mijin yake murmushi..Dubi kyakkyawar fahimta a tsakanisu. Wannan iyali za su yi nisa."

Beybey ya ce:

"Mijinta na matukar alfahari don nunata. Yana cewa tawa ce. Allah ya albarkace su gaba daya."

Gdensglam ya ce:

"Mijin na fadi a ransa tawa ce."

Kara karanta wannan

“Karin ‘Da 1 Kacal Na Nema”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ta Haifo Tagwaye, Ta Mika Masa Su a Bidiyo

omoobA777 ya ce:

"Dama mata na mikawa mazajensu albashinsu...Ban ma san nawa matata ke samu ba. Nawa dai ina samar da abubuwan bukata."

Solomon Obura733 ya ce:

"Ba zan iya tunanin ace wai ni na bukaci matata ta mika mun albashinta, baaaba girman kaina ba zai barni ba. Ita mataimakiya ce kamar yadda Allah ya fada."

Budurwa yar shekaru 19 ta tara kudi ta ginawa kanta gida mai daki 1

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar shekaru 19 ta yi bidiyon yadda ta mallaki gida nata na kanta tana da karancin shekaru.

Matashiyar (@im.moody.bby1) ta ce sai da ta tara dukka kudadenta don siyan siminti da bulo don gina gidan mai daki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng