An Rasa Rayuka Yayin da Matasa Suka Fasa Babban Siton Abinci a Jalingo
- Wasu gungun matasa sun tafka ta'asa a katafaren rumbun ajiyar kayayyaki na wani ɗan majalisa a Jalingo, babban birnin Taraba
- Rahoto ya nuna 'yan sanda da sojoji sun kawo ɗauki kuma garin kokarin tarwatsa ɓarayin suka harbe mutum biyu
- Hukumar yan sanda ta ce tana kan tattara bayanai kan ainihin abinda ya faru ranar Jumu'a da ƙarfe 11:50 na dare
Taraba - Buhunan masara da shinkafa da aka sarrafa a cikin gida na daga cikin kayayyaki na miliyoyin Naira da aka sace a wani katafaren dakin ajiyar kaya a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta ce wasu gungun Matasa ne suka kai farmaki gidan ajiyar da ke kusa da rundunar dojin 6army Brigade da daren ranar Jumu'a, 21 ga watan Yuli, 2023.
Bayanai sun nuna cewa katafaren gidan ajiyar kayan abincin mallakin wani dan majalisar jiha ne kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sardauna, a jihar Taraba.
Ɗaya daga cikin masu gadin wurin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida cewa a lokacin da matasan suka fara haduwa da misalin karfe 11:50 na dare, an sanar da sojoji da ‘yan sanda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce kafin isowar jami’an tsaro tuni matasan suka fasa rumbun ajiyar kuma suka kutsa kai ciki.
Meya faru har aka kashe mutum 2?
Mai gadin ya kara da cewa da isan jami’an tsaro wurin, sun yi harbi domin tarwatsa ɓarayin kuma garin haka ne suka harbe mutum biyu.
Kayayyakin da aka kwashe sun hada da daruruwan buhunan Masara da shinkafa da aka sarrafa a cikin gida da kuma kayan amfanin gona da suka hada da taki da maganin kashe kwari.
Haka zalika matasan ba su tsaya iya nan ba, sun shiga cikin wasu manyan siton ajiyar kayayyaki a yankin kuma sun sace kaya masu tarin yawa.
An taɓa kai hari wannan rumbun ajiyar kayan lokacin zanga-zangara EndSARS a shekarar 2020, knda aka sace kayan Miliyoyin Naira.
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Da aka nemi jin ta bakinsa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Taraba, SP Usman Abdullahi, ya ce yana kokarin tattara cikakken bayanin abinda ya faru.
Ya ce da zaran ya kammala tattara bayanai zai bayyana ainihin abinda ya faru a hukumance.
Benue: Mun Ceto Biliyan N1.2bn Daga Ma'aikatan Bogi, Gwamna Alia
A wani labarin na daban Gwamnan jihar Benuwai ya bankaɗo badakaloli a tsarin biyan ma'aikata albashi, ya ceto kuɗi kimanin biliyan N1.2 a wata ɗaya.
Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan gwamnatin Benuwai ta sanar da cewa ta gano ma'aikatan bogi 2,500.
Asali: Legit.ng