Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihohin Zamfara Da Sokoto

Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihohin Zamfara Da Sokoto

  • Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara akan ƴan bindigan da suka addabi jihohin Zamfara da Sokoto a Arewacin Najeriya
  • Dakarun sojojin sun lalata maɓoyar ƴan bindigan tare da halaka wasu daga cikinsu a wani bata kashi da suka yi da miyagun ƴan bindigan
  • Sojojin sun kuma ƙwato miyagun makamai da babura daga hannun ƴan bindigan tare da raunata da dama daga cikinsu

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' a jihar Zamfara sun fatattaki ƴan bindiga daga maɓoyarsu a ranar Juma'a.

Jaridar Channels tv ta rahoto cewa dakarun sojojin sun tarwatsa maɓoyar ƴan bindiga a ƙauyukan Mutuwa, Guda Tudu, Kawar, Dantayawa, Gidan Kare, Mahuta, da Gyado na jihohin Zamfara da Sokoto.

Dakarun sojoji sun tarwatsa ƴan bindiga a jihar Zamfara
Dakarun sojojin sun sheke 'yan bindiga hudu Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Wani babban majiya daga ɓangaren sojoji da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa dakarun sojojin sun firgita ƴan bindigan, inda suka ranta ana kare kafin sojojin su cimma su.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Arewa, Sun Halaka Da Dama Da Kwato Miyagun Makamai

Sojojin sun ƙwato babura da halaka wasu ƴan bindiga

Sai dai, dakarun sojojin sun ƙwato babura guda huɗu na ƴan bindigan inda nan take suka lalata sabuwar maɓoyar da ƴan bindigan suka gina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka kuma dakarun sojojin na 'Operation Hadarin Daji' dake a Faru cikin ƙaramar hukumar Maradun sun samu bayanan shirin ƴan bindiga na kai hari a ƙauyen Bagabuzu, rahoton VON ya tabbatar.

Nan da nan dakarun sojojin suka garzaya yankin inda suka yi musayar wuta da ƴan bindigan sannan suka hana su shiga cikin ƙauyen.

Bayan sun kammala fafatawar, an halaka ƴan bindiga huɗu yayin da sauran suka arce ɗauke da raunikan bindiga.

Sojojin sun kuma ƙwato miyagun makamai da harsasai masu yawa a hannun ƴan bindigan.

An yabawa dakarun sojojin

Haka kuma, babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yaba da jajircewar dakarun sojojin inda ya buƙace su da su ci gaba da ragargazar ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace

Ya kuma yi kira ga jama'a da su riƙa ba dakarun sojojin goyon baya ta hanyar basu sahihan bayanai kan harkokin ƴan bindigan domin tabbatar da ɗaukar matakan kare lafiya da dukiyoyi.

Sojoji Sun Ceto Mutanen Da 'Yan Bindiga Suka Sace

A wani labarin kuma dakarun sojoji masu fafatawa da ƴan bindiga a jihar Zamfara sun samu nasarar ceto wasu mutane da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su.

Dakarun sojojin sun ceto mutum tara da ƴan bindigan suka ƙwamushe bayan sun yi gumurzu da ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng