EFCC Ta Gurfanar da Tsohuwar Minista Stella Oduah Kan Zargin Wawure N7.9bn

EFCC Ta Gurfanar da Tsohuwar Minista Stella Oduah Kan Zargin Wawure N7.9bn

  • Hukumar EFCC ta maka tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
  • Ana zargin Stella da haɗa baki da wasu hadiman gwamnati da kamfanoni wajen karkatar da kuɗi kimanin biliyan N7.9
  • Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu a Kotun bayan karanta musu tuhume-tuhumen ranar Jummu'a

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa EFCC ta gurfanar da tsohuwar ministar ranar Jumu'a, 21 ga watan Yuli, 2023 bisa tuhume-tuhume 25.

Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah.
EFCC Ta Gurfanar da Tsohuwar Minista Stella Oduah Kan Zargin Wawure N7.9bn Hoto: Stella Oduah
Asali: UGC

Oduah, wacce ta riƙe ministar sufurin jiragen sama tsakanin 2011 zuwa 2014 tana fama da shari'ar zargin karkatar da maƙudan kuɗi da suka kai biliyan N7.9 tare da haɗin bakin wasu 8 da ake zargi.

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

Sauran waɗanda ake tuhuma a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CR/316/20 sun haɗa da, Gloria Odita, Nwosu Emmanuel Nnamdi, Chukwuma Irene Chinyere, da kamfanin Global Offshore and Marine Ltd.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun ƙunshi kamfanin Tip Top Global Resources Ltd, kamfanin Crystal Television Ltd da kuma kamfanin Sobora International Ltd.

Waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin da ake musu

A halin yanzu, waɗanda ake tuhuma bayan EFCC ta shigar da ƙararsu gaban mai shari'a Inyang Ekwo sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masu.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa bayan karanta masu dukkan zargin da ake musu a harabar Kotu, waɗanda ake tuhuma sun musanta hannu a badakalar nan take.

Sakamakon musanta zargin, Alkalin Kotun ya umarci waɗanda ake zargi su koma gidajensu bisa sharaɗin belin da hukumar EFCC ta ba su tun farko.

Bugu da ƙari, Kotun ta aumarci EFCC ta maida Kes ɗin ofishin Antoni Janar na ƙasar nan domin tabbatar da an gudanar da shari'ar waɗanda ake zargin yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shetimma, Gwamnoni da Sauran Mambobin NEC Sun Sa Labule a Villa, Bayanai Sun Fito

Daga na sai Alkalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 17 ga watan Oktoba, inda za a dawo a ɗora.

Gwamnoni 11 Sun Ziyarci Tsohon Shugaban APC Ta Kasa, Abdullahi Adamu

A wani labarin kuma Gwamnoni 11 na jam'iyyar APC sun ziyarci tsohon shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu a gidansa da ke Abuja.

Gwamnonin, karƙashin ƙungiyar gwamnonin APC (PGF) sun kai wa Adamu ziyara ne bisa jagorancin shugabansu kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262