Shugaba Tinubu Ya Kara Tabbatar da Kudirinsa Na Samar da Tsaro a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Kara Tabbatar da Kudirinsa Na Samar da Tsaro a Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya ƙara jaddada kudirinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sassan ƙasar nan
  • A wurin bikin yaye sojoji a Jaji, jihar Ƙaduna, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa zata ba da fifiko a ɓangaren yaƙi da masu ta da ƙayar baya
  • Ya kuma taya jami'an sojin da aka yaye murna, inda ya ayyana hukumar soji da rukuni mafi kyau a cikin miliyoyin yan Najeriya

Kaduna - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara tabbatar da kudirin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsaro mai ɗorewa a dukkan sassan ƙasar nan.

Shugaban ya sake tabbatar wa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata maida hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kowane ɓangaren Najeriya.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Kara Tabbatar da Kudirinsa Na Samar da Tsaro a Najeriya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi wannan furucin ne a wurin bikin yaye sojojin da suka kammala kwas 45 a makarantar jami'an soji da ke Jaji, jihar Kaduna, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Babu N8,000" Cikakken Jerin Garaɓasa 6 da FG Ke Shirin Raba Wa 'Yan Najeriya Don Rage Raɗaɗi

Shugaban ƙasar ya sha alwashin ƙara tallafa wa rundunar sojin Najeriya da mara musu baya kuma ya yaba musu bisa namijin kokarin da su ke yi wajen kare martabar Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika shugaba Tinubu ya taya jami'an da aka yaye murnar kammala karatu, inda ya ce ba bu kamarsu a faɗin Najeriya.

A cewarsa, jami'an rundunar soji da suka ba da rayuwarsu domin hidimta wa ƙasa sun fi kowane rukuni kyau da ƙima daga cikin adadim mutanen ƙasar nan sama da miliyan N200m.

Jami'an soji 291 aka yaye a bikin kuma an karrama su da lambar yabon Passed Staff Course. (PSC), kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tinubu ya yi sabon zubin hafsoshin tsaro a Najeriya

Wannan tabbaci daga bakin shugaban ƙasa na zuwa ne makonni kaɗan bayan ya naɗa sabbin hafsoshin tsaro da nuƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Uba Sani Ta Gano Sabuwar Cutar da Ta Ɓalle a Kaduna, Ta Faɗi Matakan da Ta Ɗauka

Shugaban ya naɗa hafsoshin tsaron a tunkurinsa na ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a tsakanin yan ƙasa musamman yankunan da ke fama da hare-hare.

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 6 a Kauyukan Jihar Benuwai

A wani rahoton kun ji cewa 'Yan bindiga sun aikata mummunan ta'adi a garuruwa biyu ranar Lahadi da daddare a jihar Benuwai.

Rahoto ya nuna maharan sun halaka rayukan mutum 6 yayin da suka kai farmaki kauyukan da ke ƙaramar hukumar Ushongo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262