Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar da Bullar Cutar Mashako a Kafanchan
- Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da ɓullar cutar Mashaƙo watau 'Diphtheria' a yankin Kafanchan, ƙaramar hukumar Jema'a
- A jiya Alhamis aka samu labarin cewa wata cuta ta ɓarke a yankin Kafanchan, har ta yi ajalin kananan yara 10
- Gwamna Uba Sani ya yaba wa ma'aikatan lafiya bisa matakin gaggawa da suka ɗauka ya kuma roki su yi duk mai yiwuwa su dakile cutar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kaduna - Gwamnatin Kaduna karkashin gwamna Malam Uba Sani ta tabbatar da ɓullar cutar 'Diphtheria' watau Mashaƙo a wasu kauyukan Kafanchan, karamar hukumar Jema'a.
Ma'aikatar lafiya ta jihar Kaduna ce ta tabbatar da ɓullar cutar bayan rahotannin da aka samu cewa mazauna gundumomin Takau, Kafanchan A da Kafanchan B sun kamu da wata sabuwar cuta.
Bayanai sun nuna cewa waɗanda suka kamu da cutar suna ganin alamu kamar numfashi da ƙyar, zazzaɓi mai zafi, tari, rashin kuzarin jiki, zafin maƙogwaro da kumburin wuya.
An Shiga Tashin Hankali Da Jimami Kan Bullar Wata Bakuwar Cuta a Jihar Kaduna, Ta Salwantar Da Rayuka
Idan baku manta ba jaridar Leadership ta rahoto cewa wata sabuwar cuta ta ɓarke a sassan Kafanchan, kuma ta yi ajalin ƙananan yara 10, waɗanda ba su haura shekara 10 ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane matakin gwamnatin Uba Sani ta ɗauka?
Sakataren watsa labaran gwamna Sani, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bayan samun rahoton rasa rayuka a yankunan, nan take mai girma gwamna ya ɗauki mataki.
A wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Jumu'a, ya ce bayan abinda ya faru, gwamna ya umarci ma'aikatar lafiya ta tura tawagar gaggawa su binciki wace cuta ce ta ɓalle.
A rahoton farko da aka tattara, ma'aikatar lafiya ta ce an samu ɓullar cutar Diphtheria karon farko a Kafanchan tun a farkon watan Yuli, 2023.
Yayin da yake yaba wa Likitoci bisa namijin kokarin da suka yi wajen kai ɗaukin gaggawa, gwamna Sani ya buƙaci su ɗora daga nan wajen tabbatar da an fattaki cutar.
Premium Times ta rahoto sanarwan na cewa:
"Matakan da ma'aikatar lafiya ta ɗauka kawo yanzu sun ƙunshi ɗaukar waɗanda suka kamu zuwa Asibitoci masu kayan aiki, binciken masu ɗauke da cutar, da wayar da kan al'umma a duk yankunan da abin ya shafa da kewaye."
Shugaba Tinubu Ya Miƙa Sunayen Ministoci Ga Majalisar Dattawa? Gaskiya Ta Bayyana
A wani labarin na daban kuma Sanata ya karyata labarin cewa sunayen ministocin shugaba Tinubu sun isa majalisar dattawa.
Umeh ya ce majalisar datttawa ba ta tattauna kan sunayen ministocin ba a lokacin da ta shiga zaman sirri domin basu ƙariso gare ta ba.
Asali: Legit.ng