Zanga-Zangar Goyon Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Man Fetur Ta Barke a Majalisar Tarayya

Zanga-Zangar Goyon Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Man Fetur Ta Barke a Majalisar Tarayya

  • Masu goyon bayan Shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur sun gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya
  • Masu zanga-zangar sun nuna amincewarsu da matakin Shugaba Tinubu na cire tallafin man fetur da aka saba da shi a ƙasar nan
  • Sun kuma nuna alfanun da cire tallafin man fetur ɗin yake da shi inda suka yi kiran da a haɗu a marawa Shugaba Tinubu baya

FCT, Abuja - Masu zanga-zangar nuna goyon bayan cire tallafin man fetur sun kawo hargitsi a ƙofar shiga harabar majalisar tarayya a ranar Alhamis, 20 ga watan Yulin 2023.

Mazu zanga-zangar sun yi nuni da cewa sun yanke shawarar fitowa kan titi ne domin nuna goyon bayansu ga Shugaba Tinubu, kan cire tallafin man fetur, cewar rahoton The Punch.

Masu goyon bayan sun barke da zanga-zanga
Zanga-zangar goyon bayan Tinubu kan cire tallafin man fetur ta barke a majalisar tarayya Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

A cewar masu zanga-zangar, Shugaba Tinubu ya yi abinda ya dace ta hanyar cire tallafin man fetur ɗin wanda ya zama ƙarfen ƙafa ga tattalin arziƙin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Shugaba Tinubu Ya Gana Da Manyan Kusoshi a Kasar Nan Domin Tsamo Talaka Daga Halin Kunci, Bayanai Sun Fito

Tinubu ya yi abin a yaba ta hanyar cire tallafin man fetur, Attah

Shugaban ƙungiyar 'Stand Up Nigeria', masu gudanar da zanga-zangar, Sunday Attah, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi abinda ya dace ta hanyar cire tallafin man fetur, sannan ta cancanci samun goyon baya domin samarwa da ƴan Najeriya romon dimokuraɗiyya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake goyon bayan cire tallafin man fetur ɗin, Attah ya yi nuni da cewa matsalar shan wahalar dogon layi yanzu ta kau inda mutane za su iya amfani da lokutansu wajen yin wasu abubuwan da suka dace.

Attah ya kuma yi kira ga ƴan adawa da masu ƙin jinin cire tallafin man fetur da su zo a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen marawa gwamnatin Tinubu baya, domin ciyar da ƙasar nan gaba.

"Ƴan adawa da masu ƙin jinin cire tallafin man fetur, su sani cewa lokacin zaɓe ya wuce kamata ya yi a haɗa kai wajen goyon bayan gwamnati ta yi abinda zai amfani ƴan ƙasa." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sunan Tsohon Gwamnan Arewa da Tinubu Ke Son Ya Zama Sabon Shugabn APC Ya Bayyana

An Ja Kunnen 'Yan Najeriya Kan Sukar Tinubu

A wani labarin kuma, kakakin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ja kunnen ƴan Najeriya kan sukar gwamnatin Shugaba Tinubu bisa tsadar man fetur da ake fama da ita.

Bayo Onanuga ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su kai zuciya nesa kan cire tallafin man fetur ɗin, inda ya ce tallafin da Tinubu ya yi alƙawarin rabawa na nan tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng