Majalisar Dattawa Ta Shiga Ganawar Sirri Kan Sunayen Ministocin Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Shiga Ganawar Sirri Kan Sunayen Ministocin Tinubu

  • Shugaban majalisar Dattawa ya shiga ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na majalisar
  • Ganawar na da alaka da sunayen ministoci da Shugaba Tinubu ya mikasa majalisar a ranar Talata
  • Ana sa ran da zarar sun kammala ganawar, Akpabio zai sanar da sunayen a yau Alhamis 20 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta shiga ganawar sirri ta gaggawa kan sunayen ministoci da ake hasashen Shugaba Tinubu ya mika.

Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana shiga ganawar ta shugabannin majalisar don tattaunawar sirri.

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan jerin sunayen ministocin da Tinubu ya mika
Majalisar Dattawa Ta Karbi Sunayen Ministocin Da Tinubu Ya Aika Mata. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa ganawar sirrin ba ta rasa nasaba da sunayen ministoci na Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban majalisar ya karbi sunayen ministocin Tinubu

Rahoton ya tabbatar da cewa hakan ya fara kawo matsaloli a majalisar wanda hakan ne ma ya tilasta shiga ganawar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Kungiya Ta Tada Jijiyar Wuya, Ta Ce Bai Kamata Tinubu Ya Ba Ganduje Da Doguwa Mukamai Ba

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karbi sunayen ministocin daga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kwanaki 50 tun bayan hawanshi karagar mulki.

Shugaban ya mika sunayen ne ta hannun magatakardar majalisar, Magaji Tambuwal a ranar Talata 18 ga watan Yuli.

A dokar kasa, shugaban nada adadin kwanaki 60 don mika sunayen ministoci, cewar Igbere TV.

Yadda Tinubu ya yi sauye-sauye a jerin sunayen ministocin

A ranar 26 ga watan Yuli ake saran wa'adin nasa zai cika kamar yadda dokar kasa ta tabbatar.

Wata majiya ta bayyana cewa an dade da kammala sunayen ministocin amma an samu tasgaro saboda wasu 'yan gyare-gyaren da aka yi a ciki.

Majiyar ta ce Shugaba Tinubu dole ya sauya wasu sunaye a jerin ministocin daga wasu jihohi a kasar.

'Yan Najeriya sun matsu su ga sunayen ministocin, amma shugaban ya bar su a duhu sai yada jita-jita ake akan wadannan za su kasance a ciki.

Kara karanta wannan

Jimami Yayin da Dan Takarar Majalisar Tarayya a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Majalisar Wakilai ta tabbatar da nadin hafsoshin tsaron da Tinubu ya mika mata don tantancewa

A wani labarin, majalisar Wakilai ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin tsaron kasar a jiya Laraba 19 ga watan Yuli.

Majalisar ta fara tantance hafsoshin tsaron ne a ranar Litinin 17 ga watan Yuli a babban birnin Tarayya, Abuja.

Shugaba Bola Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron ne a ranar 19 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.