Ana Wahala: ‘Yan Majalisa Sun Fara Kawo Hanyoyin da Talakawa Za Su Samu Ayyuka
- Francis Waive ya gabatar da kudiri a Majalisar wakilan tarayya domin a dawo da daukar mutane aiki
- ‘Dan majalisar ya ce a halin da aka shiga, kyau a janye takunkumin hana bada aiki a gwamnati
- Sanatoci sun kawo shawarar daina tambayar shekarun mai neman aiki da sunan ya ci karo da doka
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta roki Bola Ahmed Tinubu ya janye takunkumin da aka kakaba wajen daukar mutane aiki a ma’aikatun gwamnati.
A zaman ranar Laraba, Honarabul Francis Waive (APC-Delta) ya bijiro da wannan magana da majalisa ta runguma, Vanguard ta fitar da rahoton a jiya.
Francis Waive ya ce gwamnatin da ta shude ta dakatar da daukar aiki a ma’aikatu, hukumomi, cibiyoyi da kamfanonin tarayya, ya ce ya kamata a janye.
‘Dan majalisar ya nuna babu laifi yin hakan a wancan lokaci saboda tatalin arzikin kasa ya gurgunce, sannan sa’ilin ana fama da annobar COVID-19.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai karancin ma'aikata a yau
"Na tsawon shekaru ba a dauki aiki a gwamnati ba, hakan ya jawo karancin ma’aikata musamman kananan da matsakaitan jami’ai saboda mutuwa da ritaya.
Wasu sun koma hayar ma’aikatan wucin gadi, su na biyansu daga aljihunsu, ma’aikatan nan ba su da fansho kuma bai halatta a kashe kudi ba tare da kasafi ba."
-Hon. Francis Waive
Rahoton ya ce a sakamakon janye tallafin fetur, al’umma sun sake shiga kunci, saboda haka majalisa ta amince da gwamnati ta cire takunkumin.
Abba Moro yana so a daina duba shekaru
A majalisar dattawa, Sanata Abba Moro ya kawo kudirin da zai bada dama a daina amfani da shekaru a matsayin sharadi wajen daukar ma’aikata.
Sun ta ce an bijiro da kudirin ne bayan Sanatoci sun amince da aikin wani kwamitin Abdullahi Adamu da ya bukaci a cire shekaru wajen neman aiki.
Moro ya ce masu daukar ma’aikatan da ke ware shekarun wadanda za a dauka sun saba sashe na 42(2) na tsarin mulki da ya hana nuna bambanci.
Sanata Adams Oshiomhole wanda ya taba jagorantar kungiyar kwadago, bai amince da kudirin ba.
Legas za ta dauke komai
A cikin hadimai 20 da Bola Ahmed Tinubu ya nada kwanaki, an ji labari wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun ce mutum 13 daga Legas su ka fito.
Shugaban kungiyar SASG, Otunba Dele Fulani ya kawo misalin yadda aka fifita Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a kan George Akume wajen raba mukamai.
Asali: Legit.ng