Lauyoyi Sun Zargi DSS Da Musu Barazanar Rayuwarsu, Sun Bayyana Dalilin Rike Emefiele

Lauyoyi Sun Zargi DSS Da Musu Barazanar Rayuwarsu, Sun Bayyana Dalilin Rike Emefiele

  • Lauyoyin da suke kare dakataccen gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele sun zargi Hukumar DSS da musu barazana
  • Wasu daga cikin lauyoyin sun bayyana cewa hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter inda yake nuna karara nufinsu akan Emefiele
  • Sun zargi hukumar da bita da kulli ganin cewa Emefiele dan kabilar Ibo ne wanda ya kai wannan matsayi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wasu daga cikin lauyoyin da ke kare dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele sun koka kan barazanar da hukumar DSS ke musu.

Lauyoyin na kalubalantar tsare Emefiele ba bisa ka'ida ba na tsawon lokaci inda suka zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS da musu barazanar rayuwarsu.

Lauyoyi Sun Zargi Hukumar DSS Da Barazanar Rayuwarsu, Sun Bayyana Dalilin Rike Emefiele
Hukumar DSS Na Rike Da Emefiele Kan Zargin Alaka Da Ta'addanci A Kasar. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Daya daga cikinsu, Tijjani Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ke son danganta su da zargin ta'addanci, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yanzu: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Na Kwanaki 2 Kadai A Sati Bayan Cire Tallafi

Sun bayyana yadda DSS ke musu barazana

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Har zuwa karfe 6 na safe, wallafawar na nan a kafar Twitter na hukumar, kusan sa'o'i 17 kenan, kuma kowa ya gani.
"A wancan lokaci, mutane fiye miliyan biyu sun gani, yayin 3,600 suka yi sharhi, fiye da 5,000 suka yada.
"Duk da cewa mutane da dama sun yi Allah wadai da hakan, amma har yanzu rubutun na nan a shafin nasu."

Ahmed ya zargi cewa wannan kawai neman tozarta Emefiele ake son yi kakara saboda kabilanci kamar yadda Daraktan hukumar ya umarta, cewar The Guardian.

Sun fadi yadda ake son tozarta Emefiele saboda kabilanci

Ya kara da cewa:

"Wallafawar ta bayyana a fili cewa ana son tozarta Emefiele ne saboda kabilarsa kamar yadda Daraktan hukumar ya ba da umarni.
"Saboda Emefiele, a matsayinsa na dan kabilar Ibo ya kai har matsayin gwamnan babban banki hakan a wurin Bichi abin kunya ne.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

"Shiyasa suke son dankwafar da shi da zarge-zarge, a dalilinsa dukkan 'yan kabilar Ibo 'yan ta'addan IPOB da ESN ne."

“Tsarin Kudin Najeriya Ya Lalace A Karkashin Emefiele” Inji Tinubu

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa kudin kasar ya dada lalacewa ne a karkashin Godwin Emefiele.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin ganawa da 'yan Najeriya mazauna Faransa a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni.

Ya ce tsarin kudin kasar ya lalace a karkashin dakataccen gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.