Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati
- Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa Sanatoci takarda a game da nadin shugabannin hukumar NEDC
- Majalisar Dattawa ta karbi sunayen Janar Paul Tarfa (rtd) da Mohammed Alkali, za a tantance su
- An samu sabani kan wadanda za su rike NEDC da aka kafa domin mutanen Arewa maso gabas
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin majalisar dattawa a nadin shugabanni da majalisar da za ta rika sa ido a aikin hukumar NEDC.
Rahoton Daily Trust ya ce shugaban kasar ya bada sunayen wadanda Muhammadu Buhari ya ki yarda ya kara masu wa’adi ne a lokacin shi yana ofis.
Tsohon shugaban kasa Buhari bai amince da wadannan shugabanni ba, hakan ya kai ga Ministar jin kai da bada agaji, ta nada wasu shugabanni dabam.

Asali: Twitter
An yi waje da Umar Abu Hashidu
Legit.ng Hausa ta fahimci Sa’diya Farouk Umar ta zabi Umar Abubakar Hashidu a matsayin shugaban hukumar, amma bai samun yardar majalisa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mahaifin Umar Abubakar Hashidu ya yi Gwamna a Gombe tsakanin 1999 da 2003 a APP.
Rahoton ya ce sauran masu ruwa da tsaki daga Arewa maso gabas, a ciki har da Gwamnoni ba su yi na’am da mukaman ba, su ka ce ba a tuntube su ba.
Sai dai aka ji an dauke su a jirgi zuwa hedikwatar hukumar da ke Maiduguri domin fara aiki.
Janar Paul Tarfa ya dawo NEDC
A wasikar da Tinubu ya aikawa Sanatoci, Punch ta ce ya bukaci ayi amfani da sashe na 5(b) na dokar da ta kafa NEDC a 2017 a wajen tabbatar da nadin.
Shugaban kasar ya sake bada sunan Janar Paul Tarfa (rtd) ya zarce a majalisar NEDC. Tsohon sojan ya yi karatu da Buhari, ya yi ritaya ne a shekarar 1988.
Yayin da Janar Tarfa mai ritaya zai jagoranci majalisar da ke sa ido, an nemi majalisa ta sake tabbatar da Mohammed Alkali a matsayin shugaban NEDC.
Sauran wadanda ake so su koma mukamansu sun hada da Gambo Maikomo, Abdullahi Abbas, Tsav Aondoana, Mutiu Lawal- Areh da Samuel Onuigbo.
Ahmed Yahaya ne zai wakilci Gombe a matsayin Darektan gudanar da ayyuka. Sai dai mutanen jihar da-dama sun ci burin samun shugabancin hukumar.
Wasa ya rikide a APC
Da alama an fasa ba tsohon Gwamnan Kano kujerar Minista, rahoto ya zo cewa Abdullahi Umar Ganduje zai rike jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Hankalin Bola Tinubu da manyan Jam’iyya ya natsu kan Ganduje. Tsohon Gwamnan da da wasu fitattun ‘yan siyasan Osun za shiga cikin majalisar NWC.
Asali: Legit.ng