Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 40 Daga Hannun 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara
- Dakarun sojoji a jihar Zamfara sun fatattaki miyagun ƴan bindiga da suka addabi wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Bukkuyum
- Dakarun sojojin bayan fafatawa da ƴan bindigan sun samu nasarar ceto wasu mutum 40 da aka yi garkuwa da su
- Tuni dai aka sada mutanen da ake ceto a wajen ƴan bindigan zuwa ga iyalansu yayin da sojoji ke ci gaba da ƙoƙarin murƙushe ƴan bindiga a jihar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun samu gagarumar nasara kan miyagun ƴan bindigan da suka addabi jihar Zamfara.
Dakarun sojojin waɗanda aka tura ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar sun samu nasarar ceto mutum 40 da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su.
Channels Tv ta kawo rahoto cewa dakarun sojojin sun samu wasu bayanan sirri ne cewa ƴan bindigan sun sace mutane masu yawa a ƙauyukan Kyairu/Kyaram da Alkama a ƙaramar hukumar ta Bukkuyum.
Jiki Magayi: Jam'iyyar Peter Obi Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube Kan Farashin Man Fetur, Ta Fadi Abinda Zai Faru Gaba
Yadda dakarun sojojin suka ceto mutanen
Wani babban majiya daga ɓangaren sojoji da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa nan da nan dakarun sojojin suka yi shirin ko ta kwana inda suka tare hanyoyin da ƴan bindigan za su fice daga ƙauyukan Kyairu/Kyaram da Alkama a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Nan da nan ɓata kashi ya ɓarke inda aka kwashe lokaci mai tsawo ana musayar wuta da ƴan bindigan, waɗanda daga bisani aka tilasta su guduwa su bar mutanen da suka sace." A cewar majiyar.
Mutanen da aka ceto ɗin waɗanda sun kai mutum 40 an miƙa su hannun iyalansu, yayin da mutum 10 daga cikinsu an kai su wajen Sarkin Gwashi domin sada su da iyalansu, rahoton Radio Nigeria ya tabbatar.
A cikin ƴan kwanakin nan dai dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' na ci gaba da ƙara matsa ƙaimi wajen fatattakar ƴan bindigan da suka daɗe suna addabar mutanen jihar Zamfara.
Hakan na bayan kwamandan rundunar ya tabbatar da cewa ba sauran ɗaga ƙafa ga ƴan bindiga a jihar, inda ya bayar da tabbacin rundunar za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen yin maganin ƴan bindiga a jihar.
Sojoji Sun Ceto Mutum 9 a Zamfara
A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kuɓutar da wasu mutane da ƴan bindiga suka sace a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin sun ceto mutanen waɗanda yawansu ya kai mutum tara bayan sun yi mummunan bata kashi da miyagun ƴan bindiga.
Asali: Legit.ng