Wizkid Ya Ce ‘Yan Najeriya Sun Fi Damuwa Da Neman Abinci Fiye Da Yadda Suka Damu Da Siyasa
- Shahararren mawakin nan na Najeriya, Ayo Ibrahim wanda aka fi sani da Wizkid, ya bayyana dalilin da ya sa baya tsoma baki a lamuran siyasar Najeriya
- Ya ce ‘yan Najeriya sun fi mayar da hankali kan yadda za su ci su koshi fiye da yadda suka damu da siyasa
- Wizkid ya ce yana da burin ganin ya taimaki mawakan Najeriya masu tasowa domin su yi gogayya da sauran mawakan duniya
Birtaniya - Fitaccen mawakin nan na Najeriya, Ayodeji Ibrahim Balogun da aka fi sani da Wizkid, ya bayyana dalilin da ya sanya ba ya tsoma baki a harkokin siyasar Najeriya.
Wizkid ya ce ‘yan Najeriya ba su damu da wata siyasa ba, abinda suka fi mai da hakanli a kai shi ne yadda za su biya bukatun kawunansu.
Ya bayyana hakan ne a zantawar da ya yi da jaridar Evening Standard ta kasar Birtaniya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wizkid ya ki yarda ya yi sharhi a kan siyasa
Wizkid ya ki yarda ya tofa albarkacin bakinsa kan harkokin siyasar Najeriya a yayin da ake tattaunawar da shi.
Mawakin ya yi kokarin kaucewa duk wata tambaya da aka yi masa mai alaka da Shugaba Tinubu ko siyasar Najeriya.
Ya ce baya so ya ce komai kan ‘yan siyasar Najeriya, inda ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun fi damu da kawunansu da kuma abinda za su ci ba wai ‘yan siyasa ba.
Wizkid ya fadi dalilin da ya sa ya fi mayar da hankali a bangaren waka
Mawakin, wanda ya shafe sama da shekara goma yana tashe, ya kara da cewa ya mayar da hankalinsa bangaren waka ne don gujewa hayaniyar siyasa.
Wizkid ya kuma sha alwashin ganin ya taimaki sabbin mawakan Najeriya masu tasowa, wajen ganin sun yi fice a sahun mawakan duniya.
Wizkid yana cikin mawakan Najeriya da suka yi fice a duniya, domin kuwa ko a shekarar 2019, sama da mutane miliyan 240 ne suka kalli wata waka ‘Joro’ da ya dora a shafinsa na Youtube.
Momee Gombe ta yi bayani kan alakarta da mawaki Hamisu Breaker
Legit.ng a baya ta kawo muku labara, inda jaruma Momee Gombe ke bayyana cewa ba ta taba yin soyayya da Hamisu Breaker ba.
Momee ta bayyana cewa mutane ne kawai ke hasashen hakan a cikin ransu, amma babu wata alaka ta soyayya a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng