Shugaba Tinubu Ya Nada Babban Dogarin Abacha a Matsayin Shugaban DSS? Gaskiya Ta Bayyana
- Akwai bayanan da suka bayyana a Facebook da TikTok cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya shugaban hukumar DSS
- Hukumar DSS hukumar tsaro ce ta sirri wacce ta ke ɗaya daga cikin manyan hukumomin tsaron da ake da su a ƙasar nan
- A yayin da wasu a soshiyal midiya suka ce Shugaba Tinubu ya naɗa Hamza Al-Mustapha, a matsayin shugaban DSS, zancen ba gaskiya ba ne
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Batun cewa an naɗa Dr. Hamza Al-Mustapha a matsayin shugaban hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) an yi karo da shi a yanar gizo.
Al-Mustapha tsohon soja ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Alliance (AA) a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Al-Mustapha mai shekara 62 a duniya sananne ne dai a matsayin babban dogarin tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha.
Binciken gaskiya: Shin Shugaba Tinubu ya naɗa Al-Mustapha a matsayin shugaban DSS?
Batun cewa Shugaba Tinubu ya naɗa Al-Mustapha a muƙamin ya fara yawo ne a Facebook da TikTok a ranar Juma'a, 23 ga watan Yunin 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, wata mai suna Grace Idom ta rubuta a Facebook cewa:
“Bola Ahmed Tinibu ya naɗa Manjo Dr. Hamza Al'mustapha a matsayin shugaban hukumar DSS. Jagaban a shirye yake ya kai Najeriya matakin da ya dace. Muna tare da kai."
Atiku Dakur da Ahmad Muhammad Usman sun sake yin irin waɗannan kalaman a Facebook.
Sai dai, wata hukumar binciken gaskiya ta (ICIR), ta gudanar da bincike kan batun inda ta gano cewa ƙarya ne.
A bayyyane yake cewa Yusuf Bichi har yanzu shi ne shugaban hukumar DSS.
Haka kuma babu wata sahihiyar kafar watsa labarai da ta wallafa labarin har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Saboda haka, ICIR ta bayyana cewa batun cewa Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Hamza Al-Mustapha shugabancin hukumar DSS, ba gaskiya ba ne.
Shugaba Tinubu Bai Kira CJN a Waya Ba
A wani labarin kuma, jam'iyyar APC ta fito ta bayyana gaskiya kan zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kira alƙalin alƙalai kan shari'ar zaɓen shugaban ƙasa.
Jam'iyyar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya ce tsagwaronta mara tushe ballantana makama wacce ƴan adawa ke yaɗa wa.
Asali: Legit.ng