Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Za Su Raba Kudin Da Ya Fi Kowane Yawa a Tarihin FAAC

Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Za Su Raba Kudin Da Ya Fi Kowane Yawa a Tarihin FAAC

  • A sanadiyyar watsi da biyan tallafin man fetur da aka yi, baitul-malin gwamnatin tarayya ya cika
  • Kwamitin hadaka na FAAC zai yi rabon kusan Naira Tiriliyan 2 idan ya zauna a karshen watan nan
  • Da wahala idan gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun taba tara N1.95 a kwana 30

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - A karshen watan Yuli, ana sa ran Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi za su raba dukiyar da ta kai Naira tiriliyan 1.959.

Kwamitin FAAC zai yi rabon kudin da watakila ba a taba samun irinsa a tarihi ba, wannan labari ya fito a wani rahoto da ya kadaita ta The Cable.

A Mayu da Yuni, abin da su ka shigo asusun FAAC Naira biliyan 655.93 ne da Naira biliyan 786.161.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Gwamnonin jihohi Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Yadda ake rabo a kwamitin FAAC

Kara karanta wannan

Ingila Na Shirin Karbewa Tsohon Gwamnan Najeriya Naira Biliyan 100 a Kotu

Kwamitin FAAC da ke zama a birnin tarayya Abuja, yana kasa abin da gwamnatin Najeriya ta tara ne a wata na gaba, a Yuli a ke rabon kudin Yuni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai yadda ake bi wajen raba wadannan kudi da aka samu. Gwamnatin tarayya, da jihohi musamman masu arzikin mai su ka fi kaso mai tsoka.

Daga kudin shiga aka samu Naira tiriliyan 1.7 a wannan karo, sai Naira biliyan 293 ya fito daga harajin VAT sai Naira biliyan daga tura kudi ta salula.

A karon farko a tarihin Najeriya?

Jaridar ta na kyautata zaton ba a taba samun wani lokaci a tarihi da a cikin wata guda aka raba dukiyar mai yawa sosai da ta kai Naira tiriliyan 1.7 ba.

Abin da ya jawo hakan shi ne gwamnatin tarayya ta cire tallafin fetur, ma’ana an huta da biyan makudan kudi ga kamfanoni domin mai ya yi araha.

Kara karanta wannan

Attajiran Najeriya, Dangote, Rabiu, Adenuga Sun Rasa Sama Da N423bn Cikin Awanni 24 Kacal

Watakila kwamitin na FAAC ya canza farashin kudin kasar wajen da zai rika lissafi da shi a sakamakon tashin Dala daga N436 zuwa kusan N780 a yau.

Ministar kudi, tattalin arziki da takwarorinta a jihohi su na cikin ‘yan kwamitin, haka zalika manyan sakatarorin ma’aikatun da duk Akanta Janar.

Za a binciki daukar aiki

‘Yan kwanaki kadan da rantsar da ‘yan majalisar tarayya, a makon nan labari ya zo cewa sun fara shirin yin bincike na musamman kan daukar ayyuka.

An dade ana zargin tsohuwar gwamnati da nuna son kai, yanzu an samu damar bankado gaskiya. Za ayi bincike kan duk wadanda aka dauka aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel