Gwamnan Jihar Zamfara Ya Sanar Da Ranar Laraba a Matsayin Ranar Hutu a Jihar
- Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, a matsayin ranar hutu domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci
- Sanarwar gwamnan ta bayar da hutu a irin wannan ranar al'ada ce wacce aka saba a jihar domin murnar zagoyowar shekarar musulunci
- Lawal, a cikin wata sanarwa ta hannun, Abubakar Muhammad Tsafe, ya buƙaci al'ummar jihar da su yi addu'ar dawowar zaman lafiya a jihar da Najeriya baki ɗaya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Gusau, Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu, domin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Sanarwar na zuwa ne biyo bayan al'adar gwamnatin jihar ta bayyana ranar 1 ga watan Muharram na kowace shekara a matsayin ranar hutu a jihar, rahoton TVC ya tabbatar.
Gwamnan Zamfara ya ci gaba da al'adar jihar
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da darektan ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Abubakar Muhammad Tsafe, ya rattaɓawa hannu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar sanarwar, gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya buƙaci jama'ar jihar da su gudanar da adddu'o'in dawowar zaman lafiya a ƙasa a wannan lokacin.
Gwamna Lawal ya yi wa al'ummar Musulmai barka da shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Idan ba a manta ba dai, mai martaba Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III, ya sanar da ranar Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya sanar da ranar Laraba ne a matsayin 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah, sakamakon rashin ganin jinjirin watan a ranar Litinin 29 ga watan Dhul Hijjah, wanda hakan ya sanya ranar Talata ta zama 30 ga watan Dhul Hijjah, 1444.
Ranar Laraba Ta Zama Ranar Hutu a Jihar Osun
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Osun Ademola Nuruddeen Jackson Adeleke, ya sanar da ranar Laraba a matsayin ranar hutu a jihar ta Osun.
Gwamna Adeleke ya bayar da sanarwar ne domin murnar zagayowar sabuwar shekarar musulunci ta 1445 bayan Hijirah.
Asali: Legit.ng