Karin Farashin Man Fetur: Jam'iyyar Labour Party Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube

Karin Farashin Man Fetur: Jam'iyyar Labour Party Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Shagube

  • Jam'iyyar Labour Party (LP) ta ƙara yin fami kan ciwon da yake addabar ƴan Najeriya a dalilin ƙarin farashin man fetur
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa wannan wahalar da ƴan Najeriya su ke sha somin taɓi ne kan abinda zai biyo a ƙarkashin mulkin gwamnatin APC
  • Sai dai, jam'iyyar ta nuna ƙwarin gwiwarta cewa abubuwa za su daidaita a ƙasar nan inda ta buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar Labour Party (LP) ta bayyana cewa ƙarin farashin man fetur kaɗan ne daga cikin wahalhalun da ƴan Najeriya za su fuskanta a ƙarƙashin mulkin gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress), rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Kakakin jam'iyyar Obiora Ifoh, a ranar Talata da daddare ya bayyana cewa tun da farko sai da suka gargaɗi kunnen ƴan Najeriya cewa wannan gwamnatin dama masu arziƙi kawai za ta ƙarawa ƙarfi ta gasawa talakawa aya a hannu.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

Jam'iyyar Labour Party ta yi magana kan karin farashin man fetur
Jam'iyyar LP tace 'yan Najeriya za su ji a jika a mulkin Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A kalamansa:

"Kun bayar da N8000 ga iyalai masu mutum biyar sannan kun tatse duk abinda suka tara ta hanyar wasu tsare-tsaren mugunta. Ƴan Najeriya basu cancanci abinda su ke samu ba daga wajen gwamnatin nan."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jam'iyyar Labour Party ta yi Allah wadai da halin da gwamnatin nan ta ke nunawa mutanenta. Hakan na zuwa ne kuma a lokacin da gwamnatin ta zura ido tana kallon darajar naira na ci gaba da faɗuwa ƙasa warwas."

Sai dai, kakakin ya nuna ƙwarin guiwarsa cewa za ta magance dukkanin matsalolin da ta ke fuskanta sannan ƴan Najeriya za su dara nan bada daɗewa ba.

Kalaman na kakakin jam'iyyar ta Labour Party na zuwa ne bayaan farashin man fetur ya yi tashin gwauron zaɓi zuwa N617 kan kowace lita a ranar Talata, cewar eahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Dau Zafi Kan Karin Farashin Kudin Man Fetur, Ta Ba Shugaba Tinubu Muhimmin Umarni

Kungiyar Kwadago Ta Yi Magana Kan Karin Kudin Man Fetur

A wani labarin kuma, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta nuna ɓacin ranta kan yadda aka ƙara kuɗin man fetur a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana cewa sam ƙarin ba abinda ƴan Najeriya za su aminta da shi ba ne, inda ta yi Allah wadai da halin da ƙuncin da ake jefa ƴan Najeriya a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng