An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

  • ‘Yan Majalisar wakilan tarayya za su yi binciken zargin rashin adalcin da aka yi a rabon mukamai
  • Majalisa ta na zargin ana yin son kai wajen daukar aiki da raba kujerun siyasa a gwamnatin tarayya
  • Hakan ya jawo aka bukaci FCC ta kawo sunayen duk wanda aka ba mukami daga 2015 zuwa 2023

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta bukaci hukumar FCC ta gabatar mata rahoton duka mukaman da aka bada a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Da an kafa kwamitin kula da daidaito wajen ayyuka da albarkatun kasa, The Cable ta ce za a gudanar da bincike na musamman kan tsohon shugaban kasar.

Binciken da za a gudanar zai fara ne daga 2015 zuwa 2023, sa’ilin Muhammadu Buhari yana ofis.

Buhari
Majalisa za ta binciki Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Kudirin Hon. Paul Nnamchi

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

An tsaida wannan magana ne a majalisar wakilan kasar a ranar Talata bayan da ‘yan majalisar su ka amince da kudirin Hon. Paul Nnamchi (LP, Enugu).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nnamchi ya ce akwai bukatar FCC ta gudanar da aikinta yadda doka ta tanada, hakan zai bada dama ayi wa kowane yanki adalci a rabon mukamai.

A halin da ake ciki, ‘dan adawan yana ganin hukumar tayi watsi da nauyin da yake wuyanta a dokar kasa, ta koma rikicin Kwamishinoni na cikin gida.

Punch ta rahoto ‘Dan majalisar yana cewa aikin FCC ne ta sa ido kuma ta tabbata ana bin dokar daidaito idan an tashi raba wasu mukamai da damammaki.

Akwai rashin adalci a Najeriya?

Shekaru da kawo dokar, ‘dan majalisar yana ganin ba daidai ake kason damammakin aikin gwamnati, tattalin arziki, aikin jarida da kuma kujerun siyasa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Shugaban APC Ya Hakura da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Kujerarsa

Duk da abin da doka ta gindaya a kundin tsarin mulkin 1999, Hon. Nnamchi ya na zargin akwai wani bangaren da aka rika fifita wajen aikin gwamnati.

Premium Times ta ce mafi yawan ‘yan majalisa sun amince kwamitin ya yi binciken da Benjamin Kalu ya jefa tambaya domin ra'ayinsu a zamansu na yau.

Ben Kalu ya jagoranci zaman da aka yi a majalisar a madadin shugabanta, Tajuddeen Abbas.

An nade masu bada shawara a Kano

Rahoto ya zo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Mai bada shawara a kan sha’anin ciniki da wasu Hadimai 14 da za su rika taimaka masa a ofis.

Rt. Hon. Isyaku Ali Danja zai rika ba Gwamnatin Kano shawara kan harkokin majalisar dokoki, Usamata Salga zai taimakawa Abba a sha'anin addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel