Cire Tallafin Mai: An Shawarci Tinubu Ya Kara Kudin Tallafi Zuwa N30,000 Madadin N8,000

Cire Tallafin Mai: An Shawarci Tinubu Ya Kara Kudin Tallafi Zuwa N30,000 Madadin N8,000

  • Tsohon shugaban ma'aikatan gwamnan Imo, Uche Nwosu ya ba wa Shugaba Tinubu kan kudaden da za a raba
  • Nwosu ya bayyana haka ne ga 'yan jaridu a ranar Talata 18 ga watan Yuli a Abuja
  • Ya ce idan ana so kudaden su je inda ya dace, dole a saka ido sosai kada su fada hannun 'yan siyasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An shawarci Shugaba Tinubu da ya kara kudin tallafi zuwa N30,000 madadin N8,000 da ya yi niyya.

Tsohon shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Imo, Uche Nwosu ne ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu a Abuja.

Radadin Tallafi: An Shawarci Tinubu Ya Kara Kudin Zuwa N30,000 Don Isa Ga Kowa
Shugaba Ahmed Bola Tinubu Ya Ware N500bn Don Rage Radadin Cire Tallafi. Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Nwosu.
Asali: UGC

Ya bukaci shugaban da ya tabbatar an gudanar da rabon cikin tsari kada ya koma aljihun wasu daban.

Ya roki Tinubu ya kafa kwamiti don kula da rabon tallafin

Kara karanta wannan

Renewed Hope ko Wahala: An fara dawowa daga rakiyar Tinubu kan tashin kudin fetur

Ya kuma roki Tinubu da ya kafa kwamiti da zai hada da kungiyar kwadago da na dalibai da 'yan kasuwa da kuma manoma, Vanguard ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce saka wadannan kwamitin zai taimaka wurin tabbatar da anyi abin da ya dace.

Ya ce:

"Farko za mu godewa shugaban kasa da ya kara kudin daga N5,000 na tsohon shugaban kasa zuwa N8,000.
"Abu mai mahimmanci shi ne wadannan kudade an samar da su ne ba don masu abin yi ba.
"Idan muka ce kudin ba inda za su je, kenan ba mu mutunta wadanda ke barar N5 ba a kan tituna.
"Duk da haka, ina rokon shugaban ya kara kudin zuwa N30,000 yadda mata 'yan kasuwa za su samu jari.

Ya ba da shawarar yadda tallafin zai isa ga kowa

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Ya ce idan ana so tallafin ya yi tasiri dole a saka ido sosai don tabbatar da ya isa inda ake so, The Sun ta ruwaito.

A cewarsa:

"Muna kira ga shugaban ya saka ido kan yadda za a raba wannan tallafi, yin adalci a rabon shi ne abu mafi muhimmanci.
"Bai kamata a bar wadannan kudade su shiga aljihun masu ruwa da tsaki ba, a kullum irin wadannan su suke lalata lamarin kasar, da zarar kudaden sun shiga hannunsu shikenan babu mai samu."

“8k Almajirantar Da Kasar Za Ta Yi”: Shehu Sani Ya Fadi Abin Da Mutane Za Su Yi Kafin Karbar Tallafin Tinubu

A wanio labarin, tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya shawarci mutane da suyi addu'a kafin karbar kudin tallafi na Tinubu.

Shehu Sani ya ce wannan kudade babu abin da za su yi sai almajirantar da kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.