Fursunoni 5 Sun Kammala Digiri A Gidan Yarin Najeriya, Fiye Da 200 Sun Yi Rijista Da Jami'ar NOUN
- Hukumar gidan gyaran hali a Najeriya ta bayyana cewa fursunoni biyar sun kammala digiri a gidan yarin Kuje
- Kwanturola na gidajen yarin a Najeriya, Haliru Nababa shi ya bayyana haka a ranar Litinin 17 ga watan Yuli a Abuja
- Nababa wanda ya samu wakilcin shugaban gidan yarin Kuje ya ce fursunonin sun yi abin a yaba a tsakanin 'yan uwansu
FCT, Abuja - Akalla fursunoni biyar ne suka kammala digiri yayin zamansu a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Tarayya, Abuja.
Kwanturola na gidajen gyaran hali a Najeriya, Haliru Nababa shi ya bayyana haka a jiya Litinin 17 ga watan Yuli, Legit.ng ta tattaroLegit.ng ta tattaro.
Nababa wanda shugaban gidan yari na birnin Tarayya, Ibrahim Idris ya wakilta, ya ba wa fursunoni biyar takardun shaidar kammala digiri.
Ya ce fursunoni fiye da 200 sun yi rijista don ci gaba da karatu
Ibrahim ya ce fursunonin sun kammala digiri din ne a jami'ar Open University ta Kasa (NOUN), Punch ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nababa ya ce ya na da tabbacin za su fafata da sauran 'yan Najeriya ba tare da nuna musu wariya ba.
Ya ce a yanzu haka fursunoni fiye da 200 sun yi rijista da jami'ar don ci gaba da karatu a gidan yarin, cewar The Sun.
Ya godewa jami'ar NOUN saboda goyon bayan da suke ba wa gidajen yari
A cewarsa:
"Ilimi shi ne kinshikin ci gaban ko wace al'umma, don haka da wadannan takardun shaidar za su fafata da sauran 'yan Najeriya ba tare da nuna wariya ba.
"Muna kara godewa jami'ar NOUN saboda irin goyon bayan da suke ba wa gidajen gyaran hali a Najeriya ta hanyar inganta rayuwar fursunoni ta fannin ilimi.
"A yanzu haka fursunoni fiye da 200 sun yi rijista a makarantun gaba da sakandare a wannan gidan gyaran hali na Kuje kadai."
Ya kara da cewa:
"Muna kira ga sauran fursunonin da ke gidan gyaran hali na Kuje, da su yi amfani da damar da suke da shi don ganin sun inganta rayuwar su bayan an sake su."
Hukumar Gidajen Gyaran Hali Ta Sanar Da Mummunan Lamarin da Ya Faru A Gidan Yarin Kuje
A wani labarin, Hukumar gidajen gyaran hali ta Kuje ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin fursunoninta.
Rahotanni sun ce marigayin wanda ya shiga gidan yarin a shekarar 2019 ya gamu da ajalinsa ne bayan matsanancin rashin lafiya.
Yayin da aka sanya mamacin a karkashin kulawa ta musamman ta tawagar masana kiwon lafiya a magarkamar inda ake duba lafiyarsa.
Asali: Legit.ng