Lauyoyi 60 Sun Yi Taron Dangi, Za Ayi Shari’a da DSS a kan Godwin Emefiele
- Wata kungiyar masu kare hakkin Bil Adama da Lauyoyi ta shiga cikin shari’ar Godwin Emefiele
- Lauyoyin sun je kotu domin fito da Tsohon Gwamnan CBN da hukumar DSS ta cafke tun kwanaki
- An zargi Yusuf Magaji Bichi wanda shi ne shugaban hukumar DSS da laifin yi wa kotu rashin kunya
Abuja - Lauyoyin tsarin mulki da masu kare hakkin Bil Adama har 60 su ka je kotun tarayya mai zama a garin Abuja domin yin karar hukumar DSS.
Leadership ta ce wadannan Lauyoyi sun shigar da kara a kan shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi saboda cigaba da rike Godwin Emefiele.
Lauyoyin sun zargi jami’an tsaro da sabawa umarnin da kotu su ka rika yi game da tsohon Gwamnan babban bankin na CBN da yake hannunsu.
An mika kara a kotun tarayya
Maxwell Opara da Ahmed Tijani su ka jagoranci karar, su na neman Alkali ya daure Yusuf Magaji Bichi a gidan yari har sai ya wanke kan shi daga zargi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Lauyoyin, hukuncin Alkali A. Hassan, Hamza Muazu da na Bello Kawu duk sun bukaci a fito da Emefiele, amma kuma DSS ta nuna kunnen kashi.
Rahoton ya ce Opara da Tijjani sun tuhumi Gwamnatin tarayya da tsare tsohon Gwamnan na CBN duk da har yanzu ba a samu wata hujjar cafke shi ba.
Shugaban DSS zai tafi kurkuku?
Da yake magana da manema labarai bayan shigar da kararsu a jiya, Barista Opara ya ce kungiyarsu za ta tsaya tsayin-daka har sai ta ga Bichi ya tafi kurkuku.
Lauyan yake cewa hakan zai zama darasi ga sauran shugabannin hukumomin tsaro da jami’an gwamnati da ke raina kotu, su na wuce gona da iri a ofis.
The Cable ta ce kungiyar Lauyoyin da masu kare hakkin Bil Adama ta soki yadda DSS ta ke zargin Emefiele da mallakar wata bindiga da aka yi wa rajista.
Zargin da kungiyar ta ke yi shi ne ana tsare tsohon Gwamnan babban bankin ne saboda manufar siyasa, ta bukaci a gaggauta bin umarnin kotu har uku.
Duk da wannan barazana da ake yi wa shugabanta, DSS ba tayi magana a kan shari’ar ba tukuna.
Umarnin da kotu ta ba DSS
A baya, labari ya zo cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba jami'an DSS umarnin sakin Godwin Emefiele cikin gaggawa, amma ba ayi hakan ba.
Alkali ya ce cigaba da tsare shi da yi masa tambayoyi ya saɓawa ƙa'ida. Dama can Emefiele ya nemi kotun ta jingine tuhumar da hukumar DSS ta ke yi masa.
Asali: Legit.ng