Budurwa Ta Kadu Bayan Ta Biya Kudin Haya N500k Ashe Ya Siyar Da Gidan Ya Bar Kasar, Ta Nemi Mafita
- Wata budurwa ta shiga halin ni ‘yasu bayan mai haya ya tsere mata da kudi har N500,000 na watanni biyu
- Budurwar ta ce ta kama hayan gidan ne a wurin mai gidan ashe ba ta san ya siyar da gidan ba ya tsere kasar ketare
- Ta nemi shawari a kafar Twitter inda mutane da dama suka ce ai tana da ‘yancin ci gaba da zama a gidan har sai kudinta ya kare
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata budurwa a Najeriya ta sha mamaki bayan ta biya makudan kudade na haya, ashe ba ta sani ba an siyar da gidan.
Budurwar ta biya N500,000 amma kafin ta shiga an siyar da gidan kuma mai gidan ya dade da barin kasar, cewar Legit.ng.
Matar ta nemi shawara a kafar sada zumunta, yayin da Wizarab ya wallafa a kafar Twitter.
Ta nemio shawarar yadda za ta samu kudin hayanta
Ta nemi shawarar ko akwai yadda za ta yi kara don samun kudadenta, kamar haka:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Kawata ta biya N500,000 na hayar gida watanni biyu, amma ba ta sani ba ashe mai gidan ya yi niyyar siyar da gidan, yanzu haka ya siyar da komai kuma ya bar kasar gaba daya bayan karbar N500,000.”
Mutane da dama masu ta’ammali da kafar Twitter sun tofa albarkacin bakinsu bayan ganin wannan sako.
Martanin mutane a kan korafin budurwar:
@Cjamespeaks:
“Sabon mai gidan shi zai mallaki dukkan komai har da asara, za ta ci gaba da zama.”
@scamdamp:
“Ta na da daman ta zauna a gidan har na tsawon kudinta, har ila yau, mai gidan zai ba ta lokacin da za ta tashi a gidan bayan kudinta ya kare.”
@amjustcommoner:
“Shin tsohon mai gidan ya tafi da gidan ne?”
@mindx:
“Sabon mai gidan shi zai dauki komai har da asara, ta na da damar zama a gidan har sai kudinta ya kare ko kuma mai gidan ya bata sauran kudinta ta fita.”
'Ka Yi Sha'anin Gabanka': Mai Gida Ya Gargadi Mai Haya Da Ya Bar Kula Matarsa
A wani labarin, Wani dan haya ya sha mamaki yayin mai gidan haya ya saka masa dokoki akan matarsa daga shigansa gidan bai ko dade ba.
A wani sakon sirri da aka wallafa a Twitter, mutumin ya ce mai gidan hayan ya ce masa kada ya kuskura ya sake gaishe da mai dakinsa.
Mai gidan ya na zargin kaman akwai wata alaka a tsakaninsu ta soyayya ganin yadda suke gaisawa.
Asali: Legit.ng