Bayan Tafka Asara A 2022, Elon Musk Ya Dawo Matsayi Na 1 Da $250bn, Zuckerberg Ya Fado, Dangote Ya Kara Sama
- Aliko Dangote ya ci ribar akalla dala miliyan 272 a rana daya inda ya kwace matsayin shi na farko a Nahiyar Afirka da $16.4bn
- Elon Musk ya ci kazamin riba a cikin mako daya inda ya samu dala biliyan 11, yayin da kudinsa ya kai $250bn
- Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asara yayin da ya dawo na tara a jerin masu kudin duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Mai kamfanin Twitter, Elon Musk ya dawo matsayinsa na wanda ya fi kowa kudi a duniya bayan asarar $200bn a shekara daya.
Musk ya rike matsayin nasa ne bayan adadin kudin da ya ke da shi ya kai har $250bn a jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta sake.
Kamar yadda Bloomberg ya tattaro. Elon Musk ya samu $11bn a cikin kwanaki biyar kacal.
Musk ya yi sama, yayin da Zuckerberg ya tafka mummunar asara
Har ila yau, abokin hamayyarsa Mark Zuckerberg ya fado a matsayi na tara a jerin wadanda suka fi kowa kudi a duniya bayan asarar $1bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zuckerberg ya sauko kasan ne bayan tafka asara da ya yi a wannan Juma’a 14 ga watan Yuli 2023, cewar Legit.ng.
Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka ya kara samun daukaka inda kudinsa ya kai $16.4 bayan samun ribar $272m a ranar Juma’a 14 ga watan Yuli.
Dangote ya farfado bayan sauye-sauyen hada-hadar kudade
Dangote, wanda ya yi asarar kusan $3bn a cikin wata biyu bayan sauye-sauye da aka samu a kasuwar hada-hadar kudade ya fara dawowa hayyacinsa.
Dalilin asarar, Dangote ya yi kasa a cikin wadanda suka fi kowa kudi daga 76 zuwa 122 yayin da ya kuma rasa matsayin shi na wanda ya fi kudi a Afirka.
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak
Daga bisani Dangote bayan ribar da ya samu ya dawo matsayin shi na wanda ya fi kudi a Nahiyar Afirka inda ya sake doke dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert a farkon watan Yuni.
Dangote Ya Rasa Matsayin Wanda Ya Fi Arziki A Afirka, Dan Afirka Ta Kudu Ya Doke Shi
A wani labarin, shahararren dan kasuwa kuma mai kudin Najeriya, Aliko Dangote ya rasa matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a Afirka.
Aliko Dangote ya tafka asarar $3.4bn bayan faduwar dala a kasar Najeriya da sauran sauye-sauye.
Dan Afirka ta Kudu, Johann Rupert shi ya maye gurbin Dangote a matakin farko a jerin masu kudin.
Asali: Legit.ng