Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Babban Dan Majalisa a Jihar Enugu

Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Halaka Babban Dan Majalisa a Jihar Enugu

  • Mutanen ƙaramar hukumar Nsukka a jihar Enugu sun shiga cikin jimami da takaicin yin babban rashin ɗan su
  • Nelson Sylvester, wanda ya fito daga yankin kuma ɗan majalisa a ƙaramar hukumar an bindige shi har lahira a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli
  • An tattaro cewa ƴan bindiga sun farmake shi ne a gidansa da ke a Eha-Ulo inda suka harbe shi sosai kafin ya mutu

Nsukka, Enugu - Ƴan bindiga sun halaka Nelson Sylvester, kansila mai wakiltar mazaɓar Eha-Ulo a majalisar ƙaramar hukumar Nsukka ta jihar Enugu.

Sylvester, wanda aka fi sani da Ofunwa, an halaka shi ne a gidansa da ke a Eha-Alumonah cikin tsakar daren ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, cewar rahoton The Nation.

'Yan bindiga sun halaka dan majalisa a jihar Enugu
Rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta sha alwashin bincike kan lamarin Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, cikakkun bayanai kan kisan na shi ba su gama kammala ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Har Yanzu Bai Tare a Gidansa na Villa Ba, An Bayyana Muhimmin Dalilin Da Ya Janyo Hakan

Sai dai, wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun halaka Sylvester ne a cikin gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyin sun bayyana cewa an ji ƙarar harbin bindiga a wurin da lamarin ya auku inda suka harbe shi sosai kafin ya ce ga garin ku nan, rahoton Eons Intelligence ya tabbatar.

An tattaro cewa ɗan majalisar ya yi ƙoƙarin guduwa domin tsira da ransa, amma bai tsira ba saboda yawan harbin da aka yi masa, inda aka samu gawarsa kwance a harabar gidan da ke makwabtaka da nasa.

A dalilin aukuwar lamarin, mutanen yankin sun shiga cikin halin ɗar-ɗar inda suka koka kan kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Rundunar ƴan sandan jihar Enugu ta yi martani kan kisan ɗan majalisar

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu, DSP Daniel Ndukwe ya ce baya da cikakken bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Gaskiya Kan Batun Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Shekarar 2027

"Ba a yi min bayani ba kan wannan lamarin. Sai dai, zan bayar da bayanai bayan na kammala bincike nan bada daɗewa ba." A cewarsa.

Jami'an Tsaro Sun Cafke 'Yan Bindiga Bayan Sun Dawo Saudiyya

A wani labarin na daban kuma, jami'an tsaro sun cafke wasu da ake zargin ƴan bindiga ne da masu basu bayanai bayan sun dawo daga aikin Hajji a ƙasa mai tsarki.

Alhazan waɗanda suka fito daga wasu garuruwa a jihar Zamfara, an yi caraf da su bayan sun sauko daga jirgi a birnin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng