Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Cafke ‘Yan Bindiga Daga Dawowa Daga Hajji a S/Arabiya

Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Cafke ‘Yan Bindiga Daga Dawowa Daga Hajji a S/Arabiya

  • Jami’an tsaro su na ram da wasu da ake zargin ‘Yan bindiga ne da su ka dawo daga aikin hajjin bana
  • An kuma cafke matan mahajjatan jihar Zamfara tare da wasu wadanda ake zargi su na kai masu bayanai
  • Kamen da aka yi ya shafi mahajattan kananan hukumomin Tsafe, Zurmi, Bungudu da Shinkafi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Jami’an tsaro sun kama wasu da ba a san adadinsu ba tukuna, ana zargin cewa miyagun ‘yan bindiga da kuma masu kawo masu bayanai.

A wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, an fahimci wadannan mutane sun shiga hannu bayan sun dawo daga sauke farali a Saudi Arabiya.

Wadanda aka cafke sun fito daga garuruwan Tsafe, Zurmi, Bungudu da Shinkafi a Zamfara.

Sojoji
Sojoji na yakar 'yan bindiga a Madarounfa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mahajjatan da ake tuhuma da cewa ‘yan bindiga ne sun tafi aikin hajji tare da sauran Bayin Allah, jirginsu ya sauka a filin Sultan Abubakar III a Sokoto.

Kara karanta wannan

Farin Ciki: Sojoji Sun Kama Wasu 'Yan Kasar Waje Da Ke Kokarin Shigo Da Muggan Makamai Cikin Najeriya Maƙare A Mota

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun da abin ya faru a makon jiya, rahoton jaridar ya ce jami’an da ke magana da yawun jami’an tsaron Najeriya su ke nuna ba su san da maganar ba.

Gaskiyar magana ta fara fitowa

Majiyoyi da-dama daga kwamitin aikin hajjin Zamfara sun tabbata da haka. Maniyyan da suka fito daga Zamfara su na tashi ne ta filin jirgin Sokoto.

Mai magana da yawun bakin hukumar kula da alhazai ta jihar Zamfara, Mansur Shafi’i, bai amsa kiran ‘yan jarida domin yin bayani a kan binciken ba.

Amma wani ma’aikacin hukumar kula da alhazai ya yi magana da’yan jarida a boye, ya nuna jami’an tsaro sun tuntube su kan cafke wasu mahajattan jihar.

Bayanin wani jami'in kula da alhazai

"A lokacin da jirgin farko ya iso, sun umarce mu da mu jinkirta saukowar mahajatta. Bayan nan sai su ka bukaci mu kai su zuwa wani daki a tashar.

Kara karanta wannan

Hadiman Majalisa za su Lakume N16bn, Tinubu da Shettima za su ci Abincin N500bn

Daga nan sai mu ka hangi jami’an tsaro da wasu a fararen kaya. Jami’inmu a tashar ya bukaci mu bada wuri, jami’an tsaro za su gudanar da aikinsu.

- Majiya

Haka aka yi a jirgi na biyu, jami’an tsaro su ka dauke wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne da iyalansu daga cikin fasinjoji, aka shiga bincike a kan su.

An yi hakan ne da shugabannin kauyukan Shinkafi su ka sanar da cewa Bello Turji zai tafi hajji.

Umarnin Sufetan ‘Yan Sanda

Labari ya iso mana sabon shugaban ‘Yan Sanda ya sa an raba Aisha Muhammadu Buhari da Bello Matawalle da wasu tsofaffin Gwamnoni da dogransu.

Mopol za su daina tsare Rochas Okorocha, Ihedi Ohakim, Danjuma Goje, Iyorchia Ayu, Timipre Sylva kamar yadda Kayode Egbetokun ya yi alkawari a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng