IGP Ya Janye ‘Yan Sandan Tsofaffin Gwamnoni, ‘Yan Majalisa da Ministocin Buhari

IGP Ya Janye ‘Yan Sandan Tsofaffin Gwamnoni, ‘Yan Majalisa da Ministocin Buhari

  • Gwamnatin tarayya tayi na’am da karbe wasu ‘yan sanda da ke aikin gadin ‘yan siyasa a Najeriya
  • Hakan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan Kayode Egbetokun ya canji Alkali Baba a matsayin IGP
  • An tura takarda zuwa Hedikwatar Mopol 45 cewa a raba wasu manya da jami’an da ke ba su kariya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Gwamnatin tarayya ta janye dakarun kar-ta-kwana da ke kula da wasu muhimman mutane a Najeriya, daga ciki har da tsofaffin gwamnoni.

Punch ta ce shugaban ‘yan sanda, Kayode Egbetokun ya bada umarnin karbe masu gadin tsohon Sakataren gwamnatin tarayya da tsofaffin Ministoci.

Umarnin ya shafi wadanda su ka taba zama ‘yan majalisar tarayya da tsohuwar uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Buhari da wani ‘danuwanta.

Sabon IGP
Sufetan 'Yan Sanda tare da Nuhu Ribadu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Tsofaffin Gwamnoni, Sanatoci da Ministoci

Takardar da aka aikawa Hedikwatar Mopol 45 a birnin tarayya Abuja ya ambaci sunan tsofaffin Gwamnonin Imo, Gombe, Bauchi, Ogun da Zamfara.

Kara karanta wannan

An shiga matsi: Jerin gwamnoni 3 da suka ji tausayin talaka, sun kara albashin ma'aikata

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

P/Gazette ta ce sabon matakin da aka dauka ya shafi har da tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda da tsohon Ministan Neja-Delta da Halliru Jika.

Sauran wadanda aka karbewa dogarai sun kunshi tsofaffin Ministoci na ma’adanai, kimiyya da fasaha, ayyuka, wutar lantarki da kuma na kasafin kudi.

Legit.ng Hausa ta fahimci umarnin IGP Kayode Egbetokun ya hada da tsohon shugaban PDP na kasa watau Iyorchia Ayu da shugabar matan APC.

Takardar da aka fitar a makon nan ta ce wajibi ne ayi gaggawar aiwatar da umarnin da aka bada.

Ag. IGP ya cika alkawarinsa

A sakamakon karbe wadannan dakaru daga wajen ‘yan siyasa da masu mulki, rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta samu karin jami’an da ake bukata.

Wannan yana cikin alkawarin da Egbetokun ya dauka bayan ya zama Sufeta Janar na ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Yan Najeriya 4 Da Suka Yi Aiki Da Buhari Kuma Suka Samu Sabbin Mukamai

IGP Egbetokunya sha alwashin samar da kwararrun dakaru na musamman 40, 000 da su ka samu horaswa da kyau, wadanda za su ba al'umma kariya.

APC ta rasa shugaba na kasa

A babin siyasa, rahoto ya zo da ya nuna rikicin APC zai dauki salo na dabam yayin da Abdullahi Adamu ya rubuta takardar murabus a kan rajin kansa.

Jam’iyyun APC da PDP za su zama ba su da cikakkun shugabanni a Najeriya. Adamu ya bi sahun Mai Mala Buni, Adams Oshiomhole, John Oyegun a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng