NDLEA Ta Yi Nasarar Cafke Wata Lauya Da Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Yi Nasarar Cafke Wata Lauya Da Miyagun Kwayoyi

  • Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta bayyana nasarorin da samu bayan kama wasu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi
  • Daga cikin wadanda aka kaman akwai wata lauya mai suna Ebikpolade Helen da ta kware wajen safarar muggan muiyagun kwayoyi
  • Kakakin hukumar, Femi Babafemi shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli a Abuja inda ya ce Helen na zaune ne a Lekki da ke jihar Lagos

Jihar Lagos – Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta kama wata lauya da ta kware wajen hadawa da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Wacce ake zargin, Ebikpolade Helen ta kware wajen hade-haden miyagun kwayoyi daban-daban da suke bugar da mutane.

NDLEA Ta Yi Nasarar Cafke Wata Lauya Da Miyagun Kwayoyi
Lauyar Da Hukumar NDLEA Ta Cafke Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Jihar Lagos. Hoto: NDLEA.
Asali: Twitter

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli a Abuja ya bayyana cewa wacce ake zargin ta na zaune a Lekki da ke jihar Lagos, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Hallaka Wani Dan Kasuwa A Bauchi Bayan Sace Shi Ya Gagara

NDLEA ta ce an kama lauyar ne a Awka da miyagun kwayoyi

Mista Babafemi ya ce an kama Helen ne bayan samun bayanan sirri a Awka babban birnin jihar Anambra bayan kwace kilogiram biyar na ganyen tabar wiwi da kuma kwalaban kayan maye 12, Pulse ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Har ila yau, hukumar ta kwamushe wani matashi mai suna Abubakar Shu’aibu a ranar 13 ga watan Yuli a kan hanyar Mushin-Oshodi da ke Lagos da kwalaben ‘Kodin’ 86.

Ya kara da cewa nauyin kayan mayen da aka kwace a wurinshi ya kai lita 8.6 da aka samu a cikin motarsa mai lamba FFA 241YB, Daily Nigerian ta tattaro.

Hukumar ta kuma damke wasu mutane da miyagun kwayoyi

Babafemi ya ce hukumar ta kuma damke wasu wadanda ake zargi guda biyu, Razak Ogunbo da Adeola Idowu a ranar 11 ga watan Yuli a Ikorodu.

Kara karanta wannan

EFCC Ta Koma Kotu da ‘Dan Takaran APC Kan Zargin Damfarar Larabawa $1.3m

A cewarsa:

“A jihar Ondo, jami’anmu sun kai farmaki wani gida a Ehin-Ala a karamar hukumar Akure ta Kudu inda suka kama wani Abubakar Zayanu Gyambar mai shekaru 28.
“Sai kuma wani wanda ake zargi Henry Wilson mai shekaru 50 da aka kama a kauyen Ogume da ke karamar hukumar Ndokwe ta Yamma cikin jihar Delta da kayan maye da ya kai kilogiram 216.”

NDLEA Tayi Kama Masu Harkar Kwayoyi, An Yi Ram Da Malaman Addini

A wani labarin, Hukumar NDLEA ta yi nasarar kama wasu mutane da dama da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar har ila yau, ta kama wasu malaman addini na coci da ake zargin su da hannu a safarar kwayoyin.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an kama wata mata da take aiki a wani kamfani da suke taimakawa wajen safarar miyagun kwayoyin a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.