Ganduje, Namadi, Jonathan da Sauran Wadanda Suka Taba Rike Kujerar Mataimaki Kafin Zama Gwamnoni

Ganduje, Namadi, Jonathan da Sauran Wadanda Suka Taba Rike Kujerar Mataimaki Kafin Zama Gwamnoni

A siyasar Najeriya, mukamin mataimakin gwamna na zuwa ne da kima da gata da daukaka, amma wasu kadan ne suka samu damar zama gwamnoni jiharsu.

Ga mataimakan gwamnoni da yawa, iyayen gidajensu ba su ganin sun isa su karbi mulki bayan sun yi aiki dasu kafada-da-kafada na tsawon shekaru takwas.

Duk da haka, wasu kadan sun yi nasarar zama gwamnoni ta hanyar nuna kwazo ko gina kyakkyawar alaka da iyayen gidajen nasu.

Wadanda suka taba rike mataimaki kafin zama gwamna
Kadan daga tsoffin gwamnonin da suka taba rike mukamin mataimakin gwamna | Hoto: Goodluck Jonathan/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Seyi Makinde
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro sunayen mataimakan gwamnonin da suka gaji iyayen gidajensu har suka zama gwamnoni a tarihin siyasarsu.

1. Ibrahim Gaidam

An zabi Sanata Ibrahim Gaidam a matsayin mataimakin gwamnan jihar Yobe a ranar 29 ga Mayu, 2007, daga baya aka rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 26 ga Janairu, 2009 bayan rasuwar shugabansa, Mamman Ali, wanda ya rasu sakamakon ciwon hanta a jihar Florida ta Amurka, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin 1999 Da Aka Rantsar Suna Cikin Ganiyar Shekaru 30s

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gaidam ya kammala wa'adin marigayi Ali kuma ya sake lashe zabukan gwamna na 2011 da 2015, inda ya zama gwamna mafi dadewa a jihar - shekaru 10 ya shafe yana mulki yau.

2. Adebayo Alao-Akala

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, Adebayo Alao-Akala ya rike mukamin mataimakin gwamna Rasheed Ladoja na jihar Oyo daga watan Mayun 2003 zuwa Janairun 2006.

Ya mulki jihar Oyo na tsawon watanni 11 kafin bayan da majalisar dokokin jihar ta tsige Ladoja a ranar 12 ga watan Janairun 2006. Ladoja ya koma kan karagar mulki bayan da kotun koli ta soke tsige shi.

Akala ya tsaya takara kuma ya lashe zaben gwamna a shekarar 2007 a karkashin jam’iyyar PDP.

A 2011 ne ya sha kaye a zaben gwamnan da aka yi, inda marigayi Abiola Ajimobi na jam’iyyar ACN ya lashe zaben.

Kara karanta wannan

Jerin Takwarorin Shugaban Kasa Bola Tinubu Na 1999 10 Da Suka Mutu

3. Goodluck Jonathan

An zabi Goodluck Jonathan a mataimakin gwamna Diepreye Solomon Peter Alamieyeseigha na jihar Bayelsa a shekarar 1999, in ji BBC.

An tuhumi marigayi Alamieyeseigha bisa zargin cin hanci da rashawa a ranar 9 ga watan Disambar 2005 bayan da ya sha dakyar a Birtaniya ta hanyar shigar mata da ya yi.

Jonathan ya hau kujerar gwamna kuma bayan shekaru biyu aka tsayar da shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2007.

4. Abdullahi Umar Ganduje

Abdullahi Ganduje ya taba zama mataimakin gwamna ga Rabiu Musa Kwankwaso a jihar Kano daga 1999 zuwa 2003 da kuma daga 2011 zuwa 2015.

Ya gaji Kwankwaso, inda ya zama gwamna a shekarar 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

5. Umar Namadi

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, an zabi Umar Namadi gwamnan jihar Jigawa a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Gwamnan Legas da Wani Gwamnan Arewa a Villa

Kafin ya zama gwamna, ya kasance tsohon mataimakin gwamna a wajen wanda ya gabace shi daga 2019 zuwa 2023.

Kwararren akawun ya kuma kasance kwamishinan kudi na jihar daga 2015 zuwa 2019, inda aka yaba masa wajen tsara matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da ya taimaka wajen rage kudaden da ake kashewa wajen harkokin mulki da rance.

6. Mahmud Shinkafi

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Mahmud Shinkafi na jihar Zamfara ya gaji ubangidansa, tsohon gwamna Yerima Sani a 2007 a jam'iyyar ANPP bayan ya yi mataimakin gwamna na tsawon shekaru 8 daga 1999 zuwa 2007.

Sai dai ya sha kaye a zaben 2011 bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a 2008.

An kama motar shugaban APC a jihar Arewa, an titsie direbansa kan wani batu

A wani labarin, jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zargi rundunar ‘yan sandan jihar da gwamnatin jihar da kwace motar shugabanta, Tukur Danfulani daga hannun direbansa a Gusau babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamnan APC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 16, Ya Musu Nasiha da Su Ji Tsoron Allah

Bakar motar kirar Hilux mai lamba GUS 51 AH a cewar jam’iyyar APC, wasu ‘yan sanda da ake zargin suna da alaka da gwamnati ne suka kama ta ba tare da wani sammacin doka ba.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa, an kuma tsare direban na sa’o’i da dama ba tare da yi masa tambayoyin abin da ake zarginsa akai ba idan akwai, TVC News ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.