Wadanda Tsawa Ya Kashe Ba Masu Garkuwa Da Mutane Bane, Yan Sandan Kwara

Wadanda Tsawa Ya Kashe Ba Masu Garkuwa Da Mutane Bane, Yan Sandan Kwara

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta bayyana cewa tsawa da ake zargin ta kashe masu garkuwa da mutane ba gaskiya ba ne
  • Rundunar ta ce tsawar ta kashe wasu yara makiyaya ne da shekarunsu bai wuce 10 zuwa 12 ba a kauyen Oro-Ago da ke jihar
  • Kakakin rundunar a jihar, SP Ajayi Okasanmi shi ya bayyana haka bayan binciken faifan bidiyon don tabbatar da abin da ya faru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kwara – Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta yi karin haske a kan tsawa da ake zargin ta kashe wasu tsagera masu garkuwa da mutane a Oro Ago da ke karamar hukumar Ifelodun.

Rundunar ta bayyana haka ne a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli inda ta ce walkiyar ta yi ajalin wasu makiyaya biyu ne ba masu garkuwa da mutane ba.

Kara karanta wannan

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak

Kwara: Jami'an ’Yan Sanda Sun Karyata Jita-Jitar Cewa Tsawa Ta Kashe Masu Garkuwa
Jami'an ’Yan Sanda Sun Yi Karin Haske Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa Tsawa Ta Kashe Masu Garkuwa A Jihar Kwara. Hoto: @OsakanmiAjayi.
Asali: Twitter

Idan ba a mantaba, a makon da ya gabata wasu mazauna yankin sun bayyana cewa wadanda tsawar ta kashe mutum uku na daga cikin masu garkuwa da mutane takwas da suka addabi yankin, Daily Trust ta tattaro.

An yi zargin tsawa ta kashe masu garkuwa a yankin

Wadanda ake zargin su takwas sun kai farmaki a kananan hukumomin Iwo da Isin da ke jihar a makwanni biyu da suka wuce.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin harin, wani mai sarautar gargajiya a yankin ya rasa ransa, yayin da aka yi garkuwa da shugaban kungiyar Kiristoci na yankin, cewar Leadership.

Kakakin rundunar a jihar, SP Ajayi Okasanmi a cikin wata sanarwa bayan binciken faifan bidiyon ya ce wadanda ake zargin sun konen makiyaya ne yara ‘yan shekara 10 da kuma 12.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Hallaka Wani Dan Kasuwa A Bauchi Bayan Sace Shi Ya Gagara

Rundunar ta bayyana gaskiyar lamarin

A cewarsa:

“An tabbatar da wannan bayani ne daga mahaifin daya daga cikin wadanda suka konen, inda ya samu rakiyar shugaban ‘yan sa kai na Oro-Ago Mumini Usman da sauran shugabannin ‘yan sa kai na yankin.
“Rundunar ta na sanar da mutane cewa tsawar ta kashe yara guda biyu ne makiyaya wadanda kuma ba masu garkuwa da mutane ba ne kamar yadda aka bayyana a faifan bidiyon.”

Sai dai Ajayi bai yi bayanin yadda abin ya faru ba da ya yi ajalin wadannan yara makiyaya.

Tsawa Ta Yi Ajalin Wasu Da Ake Zargin Masu Garkuwa Da Mutane Ne 3 A Kwara

A wani labarin, wasu da ake masu garkuwa da mutane ne sun rasa rayukansu a jihar Kwara.

Ana zargin tsawa ce ta tarwatsa mutanen uku wadanda ake zargin sun addabi al'ummar yankin Oro-Ago da ke karamar hukumar Ifelodun.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Yuli a yankin Oro Ago da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.